Buhari ya fi amincewa da mata fiye da maza - Garba Shehu
Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban kasa ya fi amincewa da mata fiye da maza.
A yayin zantawa da gidan talabijin din NTA a ranar Juma'a, Shehu ya ce tsarin kudi na gwamnatin Najeriya a halin yanzu yana hannun mata ne.
Kemi Adeosun, wacce ta yi murabus sakamakon shaidar kammala bautar kasa ta bogi da kuma magajiyarta, Zainab Ahmed, sune mata biyu da suka rike ma'aikatar kudi a karkashin gwamnatin Buhari.
A yayin shirin, an tambayi Shehu ko akwai yuwuwar shugaban kasar ya kara wasu mata a cikin gwamnatinsa, wanda Shehu ya tabbatar da cewa akwai yuwuwar hakan.
"Wannan addu'a ce da kake yi kuma nima ina tayaka, ina goyon bayanka," mai tattaunawar da Shehu ya kara da cewa.
Ya kara da cewa, "Ina so ka gane cewa, dukkan ministocinsa na kudi mata ne.
"Bari in fadi wani abu, amma ina fatan ba zai saka ni cikin matsala ba, ya fi amincewa da mata fiye da maza .
"Dukkan wata amanar kudi a kasar nan, mata yake bai wa kuma suna matukar rike amincin nan. Suna kokari."
DUBA WANNAN: COVID-19: Karin mutum 182 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 8915
A cikin ministocin shugaba Buhari, bakwai daga cikin 43 ne mata.
Shehu ya kara da cewa shugaban kasa na son zama cikin yaransa a duk lokacin da yake jin nishadi. Ya kan kuma yi tattaki don tsinka jini ko atisaye.
"Shugaban kasa na kallon talabijin amma ya fi kallon tashoshin namun daji. Bai cika kallon NTA ba," yace.
"Shugaban kasa na shiga shauki idan yana wasa da kananan yara. Yana da jikoki wadanda yake matukar jin dadin wasa da su.
"Ya kan zagaye gidansa a matsayin atisaye," Shehu yace.
A wani labari na daban, gwamnatin Tarayya ta ce akwai wasu cututtuka da ke kashe 'yan Najeriya fiye da COVID-19 saboda likitoci na fargabar karabar majinyata a asibiti.
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabin kwamitin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng