Birai sun gudu da kayan gwajin COVID-19 bayan kai wa ma'aikacin lafiya hari

Wasu birai sun kai wa mai aiki a dakin gwajin kwayoyin cuta hari sun tsere da samfurin wasu mutane da za a yi wa gwajin coronavirus kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Lamarin mai ban mamaki ya faru ne yayin da biran suka kai harin a Kwallejin Lafiya ta Meerut da ke Delhi a India.

A cewar kafafen watsa labarai na kasar, dabobin sun kuma kwace samfurin gwajin COVID-19 daga hannun majinyata uku kuma suka tsere.

Daga bisani an gano daya daga cikin biran a kan wata bishiya yana tauna daya daga cikin samfurin gwajin kamar yadda Times of India ta ruwaito.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/b8321d79b9d3c8de.png
Birai sun gudu da kayan gwajin COVID-19 bayan kai wa ma'aikacin lafiya hari. Hoto daga The Nation
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe kaninsa da wuka saboda lemun kwalba

Rahoton ya kuma ce an sake daukan sabon samfurin da za ayi gwajin da shi daga majinyatan.

Wannan shine harin da dabobin suka kai wa mutane a baya bayan nan sakamakon dokar kulle da aka saka a kasar.

Duk da cewa sun dade suna adabar mutane a kasar, dokar zaman gida dole da aka saka a kasar watanni biyu da suka shude ya sa sun sake sake jiki.

Wasu rahotanni sun ruwaito cewa biran suna taruwa a wasu wurare a birnin Delhi da mutane suka saba taruwa.

A wani labarin daban, kunji cewa wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da wani yaro ke dambe da mahaifinsa a jihar Abia.

A cikin bidiyon, an hasko wani yaro mai suna Abuchi yana dambe da mahaifinsa a kofar gidansu a bainar jamaa.

An ji murya daga cikin bidiyon na yi wa yaron gargadi a lokacin da ya ke cigaba da dambe da mahaifinsa.

Wani da ke kallon abinda ke faruwa ya yi kokarin shiga tsakani domin ya raba fadan da ke tsakanin mahaifin da dansa.

Daga bisani ya tura matashin da mahaifinsa cikin gidansu.

A cewar rahotani, matashin yana fushi da mahaifinsa ne domin ya hana shi kudin cin abinci tun lokacin da aka kafa dokar kulle a jiharsu sakamakon bullar annobar coronavirus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng