Yan bindiga sun kashe mutane 13 a wani sabon hari da suka kai jahar Katsina

Akalla mutane 13 ne suka rigamu gidan gaskiya biyo bayan wani mummunan hari da yan bindiga suka kai a kauyukan karamar hukumar Faskari ta jahar Katsina.

Daily Trust ta ruwaito kauyukan da harin ya shafa sune: Unguwar Gizo, Maigora, Sabon Layi da kuma kauyen Mai Ruwa. Da tsakar dare yan bindigan suka kai harin da nufin satar shanu.

KU KARANTA: Barayin mutane sun yi awon gaba da shugaban gidan talabijin na NTA

Sai dai jama’an garin sun yi kokarin nuna musu tirjiya, inda suka sanya zare da su, daga nan aka shiga musayar wuta tsakanin miyagun da jama’a.

“A yanzun nan da nake maka magana, muna yi ma mutane 13 jana’iza, wasu mutane 7 kuma sun jikkata suna samun kulawa a asibiti, haka zalika sun harbi wani mutumi a kafa a kauyen mai ruwa.” Inji wani dan garin.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/553a37cd8719b39f.jpg
Gwamnan jahar Katsina
Source: UGC

Kakaakin rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar harin, inda yace:

“Eh da gaske an kashe mutane 13, muna yawan fada ma mutanen dake kauyukan su daina ja da miyagun nan.

“Suna amfani ne da abindigar AK-47, babu yadda za ku iya fada da su kuna dauke da bindigar toka, sun shiga ne da nufin satar shanu, amma jama’an garin suka kalubalance su, hakan yasa yan bindigan suka bude musu wuta.” Inji shi.

A wani labari kuma, miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da Chinyere Okoye, mataimakiyar manajan labaru ta hukumar gidan talabijin na kasa watau, NTA, a garin Aba na jahar Abia.

The Nation ta ruwaito an sace Chinyere ne a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu a daidai kofar gidanta yayin da take cikin motarta bayan dawowa daga wajen aiki.

Wasu majiyoyi daga rundunar Sojan kasa dake da masaniya game da aukuwar lamarin sun bayyana cewa yan bindigan sun nemi a biya su kudin fansa, amma basu fallasa ko nawa bane.

Ma’aikatan gidan sun bude mata kofa da nufin ta shigo da motar kenan sai kawai suka tarar da babu kowa a cikin motar, daga nan suka shiga halin rudani da firgici.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com