Albishir: Gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin fara daukar aikin mutum 774,000 a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana inda aka kwana a kan shirinta na daukar ma'aikata 774,000 a fadin kasar nan
- Karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo ne ya bada sanarwar
- Keyamo ya bayyana cewa shirin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Oktoba
Gwamnatin tarayya ta bayyana inda ta kwana a kan daukar ma'aikata 1,000 a kowacce karamar hukuma 774 da ke fadin kasar nan.
Karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, ya bada sanarwar a ranar Alhamis 28 ga watan Mayu, a wani taron manema labarai.
Ya ce za a fara diban aikin a ranar 1 ga watan Oktoba, Premium Times.
Gwamnatin tarayyar ta bayyana tsare-tsaren ta na samar da ayyuka ga 'yan Najeriya 774,000.
Ya ce kwamiti za a kafa wanda zai tantance wadanda za su amfana da wannan romon na gwamnatin tarayya.
Kamar yadda Keyamo ya bayyana, kwamitin ne za su kawo wa gwamnatin sunayen wadanda za a dauka aikin daga kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.
KU KARANTA KUMA: Sokoto: Yadda rayuka 270 suka salwanta a cikin hari 20
Ministan ya bayyana cewa za a fitar da adireshin yanar gizo inda wadanda ke bukatar aikin za su iya yin rijista sannan a fitar da sunayen jama'a su gani.
Keyamo ya ce wadanda za a dauka din za su dinga karbar N20,000 kowanne wata.
A wani labarin kuma, mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya karyata rahoton da jaridar Sahara Reporters ta wallafa a ranar Alhamis kan shugaba Muhammadu Buhari.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, rashin kyakkyawan yanayin hanyar sadarwa ya hana shugaba Buhari gabatar da jawabai a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar ta hanyar bidiyo domin kiyaye dokar nesa-nesa da juna.
An gabatar da taron ne kan al'amuran da suka shafi kudi da ci gaban kasa, wanda babban sakataren majalisar, António Guterres ya jagoranta.
Sai dai fa jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, rashin kyakkyawan yanayi na hanyar sadarwa da shugaban Najeriya ya fuskanta tun daga mafarar taron da aka gudanar ta hanyar bidiyo, ya sa bai samu damar cewa uffan ba.
Haka kuma jaridar ta alkanta wannan rahoto da cewa ta kalato shi ne daga rahoton da jaridar The Punch ta wallafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng