Akwai cututtukan da ke kashe 'yan Najeriya fiye da korona – FG

– Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna bacin ranta kan yadda wasu asibitocin gwamnati ke korar majinyata saboda tsoron korona

– Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce hakan ya janyo mace macen da suka fi na korona

– Mustapha ya ce ministan Lafiya na kasa, ya umurci dukan asibitocin gwamnati da masu zaman kansu su rika kulawa da dukkan majinyata bai sai masu korona ba kawai

Gwamnatin Tarayya ta ce akwai wasu cututtuka da ke kashe 'yan Najeriya fiye da COVID-19 saboda likitoci na fargabar karabar majinyata a asibiti.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabin kwamitin.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/9d7863c94d36cdf5.png
Boss Mustapha. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Sokoto: Buhari ya yi martani mai zafi a kan kisan mutum 50

Ya ce, "Lamarin ya munana duba da cewa bayanan da muka samu sun nuna har asibitocin gwamnatin tarayya suna daga cikin wadanda ke kin duba majinyata saboda tsoron COVID-19.

"Ba zamu amince da haka ba. Mun yi bakin cikin samun wannan bayanin.

"Maganan gaskiya, mun fi samun mace–mace sakamakon rashin kulawa da wasu cututtuka fiye da wadanda COVID-19 ke kashewa.

"Abinda yasa muka bawa COVID-19 muhimmanci shine saboda annoba ce da za ta iya kashe wani sashi na al'ummar mu masu yawa."

Ya ce ministan Lafiya ya bawa dukkan shugabanin asibitoci umurnin su cigaba da kulawa da sauran marasa lafiya don kare mace–mace.

Ya bukaci shugabanin asibitocin na gwamnati da masu zaman kansu su rika kulawa da masu fama da wasu cututtukan.

Ya ce akwai tsare tsaren kulawa da majinyata da ke da alamun cutar korona kuma idan aka bi dokokin da wuya wani ya harbu da cutar.

A wani labarin daban, kunji cewa wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da wani yaro ke dambe da mahaifinsa a jihar Abia.

A cikin bidiyon, an hasko wani yaro mai suna Abuchi yana dambe da mahaifinsa a kofar gidansu a bainar jamaa.

An ji murya daga cikin bidiyon na yi wa yaron gargadi a lokacin da ya ke cigaba da dambe da mahaifinsa.

Wani da ke kallon abinda ke faruwa ya yi kokarin shiga tsakani domin ya raba fadan da ke tsakanin mahaifin da dansa.

Daga bisani ya tura matashin da mahaifinsa cikin gidansu.

A cewar rahotani, matashin yana fushi da mahaifinsa ne domin ya hana shi kudin cin abinci tun lokacin da aka kafa dokar kulle a jiharsu sakamakon bullar annobar coronavirus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng