Barayin mutane sun yi awon gaba da shugaban gidan talabijin na NTA

Wasu miyagu yan bindiga sun yi awon gaba da Chinyere Okoye, mataimakiyar manajan labaru ta hukumar gidan talabijin na kasa watau, NTA, a garin Aba na jahar Abia.

The Nation ta ruwaito an sace Chinyere ne a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu a daidai kofar gidanta yayin da take cikin motarta bayan dawowa daga wajen aiki.

KU KARANTA: Gwamnati za ta bude filayen jirgin saman Kano, Legas, Abuja da Fatakwal

Wasu majiyoyi daga rundunar Sojan kasa dake da masaniya game da aukuwar lamarin sun bayyana cewa yan bindigan sun nemi a biya su kudin fansa, amma basu fallasa ko nawa bane.

Ma’aikatan gidan sun bude mata kofa da nufin ta shigo da motar kenan sai kawai suka tarar da babu kowa a cikin motar, daga nan suka shiga halin rudani da firgici.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/4ec36dfc619082b5.jpg
Yan bindiga Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Haka zalika mijinta ya kira lambar wayarta a daren Laraban don jin inda take, amma sai guda daga cikin yan bindigan ya amsa wayar, kuma ya shaida masa cewa zasu neme shi.

Sai washegari Alhamis suka sake kiransa inda suka nemi makudan kudade daga hannunsa kafin su sake ta.

Babban manajan NTA Aba, Nwadi Elobuike ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labaru, kuma ta nuna damuwarta da hakan.

Wasu yan jaridu a garin sun bayyana damuwarsu da lamarin, tare da bayyana fargabar yadda ake satar yan jaridu a jahar, wanda suka ce hakan ba zai haifar ma jahar Da mai ido ba.

Daga karshe sun yi kira ga yan bindigan su sako musu abokiyar aikinsu saboda karamar ma’aikaciya ce dake karbar albashi mara tsoka, kuma da shi take kula da iyalanta.

A wani labarin kuma, wasu tubabbun yan bindiga a jhar Zamfara sun ceto kimanin mutane 12 da wasu miyagun yan bindiga suka sace su, kuma tuni sun mika su hannun Yansanda.

Kakaakin rundunar Yansandan jahar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka, inda yace:

“Kwamitin zaman lafiya na jahar Zamfara tare da hadin gwiwar tubabbun yan bindiga sun ceto mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane. Kimanin makonni biyu da suka gabata aka yi garkuwa da mutane.

“Amma Allah Ya kubutar da su ta hannun tubabbun yan bindiga da suka kai harin kwantan bauna kan miyagun yan bindigan da suka yi garkuwa da mutanen.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com