Barden yakin kungiyar Boko Haram, Saad Karami, ya mika wuya ga rundunar soji

Barden yakin kungiyar Boko Haram, Malam Adamu Yahaya, wanda aka fi sani da Saad Karami, ya mika wuya ga bataliyar rundunar soji ta 242 da ke Monguno a ranar 24 ga watan Mayu.

Karami ne ya jagoranci tawagar mayakan kungiyar Boko Haram da ta kai hari na karshe a kan rundunar soji da garin Baga.

Dakarun rundunar soji a karkashin atisayen Ofireshon Lafiya Dole sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 12 tare da kubutar da mutane 241 da su ke rike da su a garin Mudu a jihar Borno.

Mutanen da sojojin su ka kubutar sun hada mata 105 da kananan yara 136.

Kazalika, sojoji sun sauke tutar da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kafa a garin, sannan an kwashe sauran kayan amfaninsu da ke garin.

Ba a samu asarar rai ko ta kayan aiki ba a bangaren rundunar soji yayin samamen da su ka kai garin ranar 24 ga watan Mayu domin murkushe sauran mayakan kungiyar Boko Haram

Bataliyar sojoji ta 151 da ke karamar Bama ta kai hari a yankin kwanar Banki da ke garin Firgi a karamar hukumar Bama.

Yayin harin, dakarun soji sun kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram da su ka hada da 'yan kunar bakin wake.

Jawabin hedkwatar tsaro yace: " Yahaya AKA Saad Karami ya mika wuya ga dakarun 242 bataliya a Munguno. Ya jagoranci harin garin Baga sannan ya yi musharaka ya hare-haren Metele, Mairari, Bindiram, Kangarwa da Shetimari (Kasar Nijar)."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng