Yadda wani mutum ya kashe kaninsa da wuka saboda lemun kwalba

Wani Chisom Eze ya kashe kaninsa, Henry mai shekaru 19 ta hanyar caka masa wuka lokacin da suke fada saboda lemun kwalba a gidansu da ke Johnson Street a unguwar Alaba a Legas.

Punch Metro ta ruwaito cewa Chisom mai shekaru 21 ya bar lemun kwalbansa a cikin gida ya fita domin yin wata harka amma da ya dawo sai ya tarar kaninsa Henry ya shanye lemun bayan fitarsa.

Sakamakon bacin rai da fushin abinda kaninsa ya aikata, Chisom ya dako wuka ya daba wa Henry a wuyansa.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/7a6dfa42632e4984.png
Bala Elkana. Hoto daga Punch Metro
Source: UGC

Yar uwarsu da ke gidan kuma abin ya faru a gabanta ta sanar da makwabta kuma suka kama Chisom kafin ya tsere.

DUBA WANNAN: COVID-19: Karin mutum 182 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 8915

Dukkan kokarin da aka yi na ceto ran Henry bai yi nasara ba domin ya mutu sakamakon raunin da yayansa ya masa yayin fadarsu.

Bidiyon fadar da Instablog9ja ta wallafa a shafin sada zumunta na instagram ya nuna makwabta da sauran mutane sun taro yayin da ake fitar da gawar mamacin daga gidansu.

Da aka tuntube shi domin samun karin bayani, mai magana da yawun rundunar yan sandan Legas, Bala Elkana ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce, "Chisom ya kashe kaninsa Henry ta hanyar caka masa wuka saboda lemun kwalba. A halin yanzu yana tsare a hannun mu. Muna gudanar da bincike."

A wani labarin daban, kunji cewa wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da wani yaro ke dambe da mahaifinsa a jihar Abia.

A cikin bidiyon, an hasko wani yaro mai suna Abuchi yana dambe da mahaifinsa a kofar gidansu a bainar jamaa.

An ji murya daga cikin bidiyon na yi wa yaron gargadi a lokacin da ya ke cigaba da dambe da mahaifinsa.

Wani da ke kallon abinda ke faruwa ya yi kokarin shiga tsakani domin ya raba fadan da ke tsakanin mahaifin da dansa.

Daga bisani ya tura matashin da mahaifinsa cikin gidansu.

A cewar rahotani, matashin yana fushi da mahaifinsa ne domin ya hana shi kudin cin abinci tun lokacin da aka kafa dokar kulle a jiharsu sakamakon bullar annobar coronavirus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng