Hadarin Daji: An kashe 'yan bindiga fiye da 30 a Zamfara

A kalla 'yan bindiga 30 ne su ka rasa ransu yayin wani luguden wuta da dakarun rundunar sojin sama su ka yi a dajin Doumborou da ke jihar Zamfara.

A cikin jawabin da manjo janar John Enenche, shugaban sashen yada labarai na rundunar soji, ya fitar ya ce an lalata ma'adanar makamai da sauran kayan aikin 'yan bindigar yayin ruwan wutan da sojoji su ka yi mu su.

Dakarun soji sun kai harin ne a karkashin atisayen nan mai taken HADARIN DAJI.

Jawabin ya bayyana cewa, "rundunar sojojin sama a karkashin atisayen HADARIN DAJI sun lalata dakin ajiyar kayan aikin 'yan bindigar Zamfara tare da kashe a kalla 30 daga cikinsu yayin luguden wutar da aka yi musu a dajin Doumborou ranar 26 ga watan Mayu.

"An kai hari dajin ne bayan samun sahihan bayanai ta hanyar amfani da fasahar HUMINT. Na'urori sun nuna wuraren da 'yan bindigar ke buya tare da boye kayan amfaninsu a dajin.

"Wata na'ura mai bin motsin mutane ta bi sahun wasu 'yan bindiga a kan babura har zuwa dakin da su ke adana kayan amfaninsu.

"Jirgin yaki na rundunar sojin sama ya samu nasarar lalata ma'ajiyar tare da kona wurin. Kazalika, jirgin ya bi sahun 'yan bindigar da su ka gudu tare da kashe a kalla 30 daga cikinsu," a cewar jawabin.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/vllkyt7en01ssk497.jpg
Jirgin yakin NAF
Source: Twitter

Jawabin ya kara da cewa babban hafsan rundunar soji (CAS) ya yabawa kokarin rundunar atisayen HADARIN DAJI bisa kwarewar aiki da jajircewa wajen kaddamar da hare - hare a kan 'yan bindiga.

A ranar Asabar ne gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawallen Maradun, ya ce har yanzu yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatinsa ta kulla da 'yan bindiga a jihar ba ta daina aiki ba.

Matawalle ya ce zai cigaba da girmama yarjejeniyar da gwamnatinsa ta kulla da 'yan bindigar da su ka tuba.

DUBA WANNAN: Kiyayya da keta: An kori 'yan sandan kasar Amurka 4 da su ka kashe wani bakar fata (bidiyo)

Ya kara da cewa gwamnati za ta yi amfani da karfin doka a kan 'yan bindigar da su ka ki rungumar sulhu.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, yayin da ya ke jajantawa jama'ar wasu kauyuka a kan harin da 'yan bindiga su ka ki mu su a makon jiya.

Ya mika sakon jajen ne ga jama'ar kauyukan Unguwar Rogo, Karda, Bidda da Kajera a yankin karamar hukumar Tsafe da kauyen Kabaje a yankin karamar hukumar Kaura - Namoda.

A kalla mutane 10 aka kashe tare da raunata wasu da dama kafin daga bisani jami'an tsaro su kawo dauki yayin hare - haren.

A cewar Matawalle, "ina aiki ba dare ba rana, ko barci ba na iya samu, saboda na tattauna da jami'an tsaro da sauran ma su ruwa da tsaki.

"Mun samu tabbaci daga wurin shugabannin Fulani da su ka karbi tsarinmu na sulhu a kan cewa za su tattauna da 'yan bindiga ma su kunnen kashi domin nuna mu su muhimmancin rungumar sulhu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng