Yanzu-yanzu: FG za ta bada tsare-tsaren bude makarantu
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shaida cewa za ta fitar da tsare-tsaren bude makarantun fadin kasar nan
- Shugaban kwamitin yaki da cutar korona na kasa, kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da manema labarai
- Ya yi kira ga dalibai, iyaye da duk masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan da su yunkura ta yadda gwamnatin za ta samu karfin guiwa
Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin fitar da tsare-tsaren bude makarantu a fadin kasar nan.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, shugaban kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a ranar Laraba a Abuja.
Yayin taya yara kanana na kasar nan murnan zagayowar ranarsu ta wannan shekarar, sakataren gwamnatin tarayyar ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su dauka matakan da za su taimaka wajen bude makarantu a fadin kasar nan.
Ya ce, "Ina son sanar da 'yan Najeriya cewa ma'aikatar ilimi na kokarin sakin tsare-tsaren bude makarantu.
"Kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa na amfani da wannan damar wurin taya yaranmu murna tare da tabbatar musu, iyaye da dukkan masu ruwa da tsaki cewa ana kokarin ganin an bude makarantu.
"A don haka, muna amfani da wannan damar wurin kira ga gwamnatocin jiha, kananan hukumomi da dukkan masu ruwa da tsaki da su dauka matakan da za su sa a gaggauta bude makarantu."
DUBA WANNAN: MURIC ta nemi a tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar Idi a jihohinsu
A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda a karamar hukumar Zaria sun damke malaman addinin Musulunci 3 a tsakanin Juma'a zuwa Lahadi sakamakon zarginsu da ake da jan sallar Idi da na Juma'a.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, an gayyaci malamai biyu don tuhuma tare da amsa tambayoyi a kan sallar Idin da suka ja a ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata.
Sani Halifa shugaba ne a malamai mabiya darikar Tijjaniya a garin Zaria. Ya ja sallar idi a ranar Asabar bayan umarnin shugaban darikar Tijjaniya na kasa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya tabbatar da cewa ranar Asabar ce daya ga watan Shawwal.
An gano cewa jami'an 'yan sanda sun kira tare da tuhumar malamin don ya wanke kansa. An kama wani malami mai suna Sardauna Limamin Bizara a ranar Lahadi bayan ya ja sallar Idi a kauyen Bizara da ke Zaria. An sake sa bayan tuhumarsa da aka yi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng