Kungiyar Kwadago ta ba wa Ganduje kwanaki 14 ya dawo wa da ma'aikatan Kano albashinsu da ya zaftare
Kungiyar Kwadago reshen jihar Kano, ta ba wa gwamnatin jihar wa'adin kwana 14 ta gaggauta dawo wa da ma'aikatan gwamnatin jihar albashin su na watan Mayu da ta zaftare.
A yayin da wa'adin kwanaki 14 zai kare, kungiyar ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aiki na gargadi da jan kunnen gwamnatin jihar muddin ba ta warware hukuncin da ta dauka ba.
Shugaban kungiyar na Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, shi ne ya ba da shaidar hakan yayin taron manema labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Kungiyar ta ce an zaftare albashin ma'aikatan ne kwatsam ba tare da an sanar da su ba.
A makon da ya gabata daidai lokacin da al’ummar musulmi ke shirye-shiryensu a kan bukukuwan karamar Sallah, ma’aikatan gwamnati a jihar Kano sun tsinci kansu a cikin halin rashin tabbas.
Ma'aikata a Kano sun tsinci kansu cikin yanayi na zulumi yayin da suka wayi gari gwamnatin jihar ta zaftare albashinsu ba tare da wani cikakken bayani ba.
Binciken ya nuna cewa, galibin ma'aikatan da suka fara ganin albashin daga ranar Laraba, sun koka da cewa an yanke abin da ya kai daga kashi 20 zuwa 30 cikin dari na albashin nasu.
Hakan ya sanya Kwamared Minjibir ya bayyana damuwa game da wannan mataki, lamarin da ya ce gwamnatin ba ta tuntube su game da lamarin ba kafin ta zartar da hakan.
KARANTA KUMA: Ana kyautata zaton samun maganin cutar korona daga jikin 'ya'yan Gwaiba
Sai dai a wani rahoton mai nasaba da wannan wanda ana iya dangana shi da karin maganar nan ta 'ana tauna aya ne domin aya ta ji tsoro', gwamnan Kano tun a makon da ya shude, ya sanar da cewa zai zaftare rabin albashin sa.
Kafofin watsa labarai da dama sun ruwaitio cewa, Ganduje a ranar Lahadi, 17 ga wayan Mayu, ya sanar da cewa zai datse rabin albashinsa tare da na sauran dukkanin masu rike da mukaman siyasa a jihar Kano.
Sanarwar hakan ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar, lamarin da ya ce rashin samun kudin shiga da annobar korona ta janyo ita ta tilasta wa gwamnatin Kano daukar wannan mataki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng