Da duminsa: Ize-Iyamu ya karbi takardun bayyana niyyar takara a hedkwatar APC

Zababben dan takaran gwamnan jihar Edo da wani ballin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta zaba, Fasto Osaze Ize-Iyamu ya dira hedkwatar jam'iyyar dake Abuja don bayyana niyyarsa.

Osaze ya dira hedkwatar jam'iyyar APC dake unguwar Wuse2 Abuja ne domin sayan fom na bayyana aniyar takarar zaben gwamnan jihar Edo da za'a gudanar shekarar nan.

Za'a yi zaben ne a ranar 9 ga Satumba, 2020.

Dan takaran ya isa hedkwatar misalin karfe 12 na rana tare da dimbin masoyansa kuma sun samu tarbar manyan jami'an hukumar irinsu shugaban uwar jam'iyya, Adams Oshiomole da mataimakinsa, Hillard Eta.

Za ku tuna cewa a shekarar 2016, Osaze Ize-Iyamu ya yi takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, inda ya sha kaye hannun Godwin Obaseki na APC.

Mai magana da yawunsa, John Mayaki, ya bayyana cewa Ize Iyamu ya shirya tsaf domin kwace kujerar gwamnan daga hannun wanda ke kai yanzu.

Yace: "Ta hanyar karban wannan fom din yai, mun dinke matsayinmu kan takardar kuri'ar jam'iyyarmu a zaben fidda gwanin da za'a gudanar watan gobe (22 ga yuni)."

"Wannan babban nasara ne kuma muna godiya ga dukkan yan takaran da suk rakomu nan yau domin nuna goyon baya."

KU KARANTA: Amnesty ta bukaci a saki dan jaridar da ya soki Lai Mohammed

Gabanin karbar takardar, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Fasto Osagie Ize-Iyamu ya zama zababben dan takarar kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ize-iyamu, wanda ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Edo, ya zama dan takarar ne a ittifakin da jigogin jam'iyyar suka yi a daren Talata a Abuja.

Shugaban kwamitin tantance yan takarar, Sanata Francis Alimikhena, ya gabatar da Faston a matsayin wanda ya wakilci jam;iyyar a zaben.

Sauran mambobin kwamitin tantancewar sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Lucky Imaseun; Janar Ceci Esekhaobe, Thomas Okosun, Samson Osagie, Patrick Obahiagbon da Peter Akpatason.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng