Yanzu-yanzu: An doke gwamnan jihar Edo a zaben fidda gwanin APC

Fasto Osagie Ize-Iyamu ya zama zababben dan takarar kujerar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ize-iyamu, wanda ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar EDo, ya zama dan takarar ne a ittifakin da jigogin jam'iyyar suka yi a daren Talata a Abuja.

Shugaban kwamitin tantance yan takarar, Sanata Francis Alimikhena, ya gabatar da Faston a matsayin wanda ya wakilci jam;iyyar a zaben.

Sauran mambobin kwamitin tantancewar sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Lucky Imaseun; Janar Ceci Esekhaobe, Thomas Okosun, Samson Osagie, Patrick Obahiagbon da Peter Akpatason.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/68f5f57035952e82.jpg?imwidth=900
Osaze Iyamu
Source: UGC

KU KARANTA: Amnesty ta bukaci a saki dan jaridar da ya soki Lai Mohammed

Gabanin yanzu, an samu mumunan sabani tsakanin shugaban uwar jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, wanda ya kai ga sukayi hannun riga.

Obaseki ya zargi Oshiomole da kokarin kawowa mulkinsa cikas ta hanyar yunkurin juyashi kamar yaronsa.

Rikicin ya bayyana ga jama'a ne lokacin da ake shirin yi zaben shugabannin majalisar dokokin jihar inda masu biyayya ga Oshiomole suka yi mabiya gwamnan rinjaye.

Da gwamnan ya fuskanci hakan sai ya sa aka gudanar da zaben cikin dare inda yan majalisa 9 kadai kuma masu goyon bayansa suka halarta. Tun lokacin sauran 13 suka daina zuwa majalisa.

A ranar Laraba, gwamna Godwin Obaseki, ya bayyanawa tashar Channels cewa babu ma'alukin da ya isa ya hanashi zarcewa a kujerarsa na gwamna.

Yace: “Ni ba mai son tada rigima ba ne. Amma ina da tabbacin yadda na zama gwamna, haka zan koma kan kujera."

“Ubangiji ya ba ni mulki. Idan Ya na so in koma gwamna, zan cigaba. Babu mutumin da ya isa ya taka mani burki.”

A yanzu haka, abokin hamayyarsa Fasto Osaze Ize-Iyamu ya garzaya hedkwatar jam'iyyar APC dake birnin tarayya Abuja domin karbar takardar dan takara gwamnan kujeran gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng