Kallo ya koma sama: An tsinci gawar dan uwan dan majalisa cikin sundukin mota
Dan majalisa mai wkailtar mazabar Ebonyi ta Arewa maso yamma, Victor Aleke ya yi rashin dan uwansa, kaninsa uwa daya uba daya a wani yanayin mutuwa mai daukan hankali.
Premium Times ta ruwaito an tsinci gawar mamacin mai suna Samuel Aleke ne a sashin ajiyen kaya, watau ‘boot’ din motarsa a kan babbar hanyar Abakaliki zuwa Afikpo na jahar Ebonyi.
KU KARANTA: Tsuntsu daga sama gasashshe: PDP ta fara zawarcin babban gwamna a jam’iyyar APC
Rahotanni sun bayyana mamacin ya fita gida ne a ranar Asabar 23 ga watan Mayu da yamma, amma daga nan ba’a sake jin duriyarsa ba, har sai washe gari da aka tsinci gawarsa.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa mamacin ya shaida ma matarsa cewa za shi ya karbo na’aurar jin magana na kunne ne daga wajen wani abokinsa.
Wannan shi ne gani na karshe da iyalansa suka masa, inda bayan daukan tsawon lokaci suna jiran dawowansa sun ji shiru, sai matar dake dauke da juna biyu ta yi shela aka fara nemansa.
Koda aka gano gawar, an tarar da rauni a fuskarsa da kuma bayansa, wanda hakan ke alanta hari aka kai masa, kuma tuni aka sanar da hukumar Yansandan jahar don gudanar da bincike.
Ita ma kakaakin hukumar, Loveth Odah ta tabbatar da lamarin, inda ta ce Yansanda ne suka gano gawar, kuma tuni sun mika gawar zuwa wani dakin ajiyar gawa domin binciken lamarin.
A wani labarin kuma, Mutum 1 ya mutu, da dama sun jikkata a wasu hadarurruk biyu da suka faru daban daban a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.
Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito shugaban hukumar kare haddura reshen jahar Ogun, Clemet Oladele ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a garin Ogun a ranar Litinin.
Oladele yace hadarin ya kunshi maza 2 da mace 1, inda motar ta kufce madirebanta sakamakon halin maye da yake ciki, wanda yasa ya yi ta gudun wuce sa’a a kan titin har ta kufce masa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com