An gano abinda ya haddasa barkewar Cacar baki tsakanin Pantami da hukumar NiDCOM
A yayin da bayanai ke kara fitowa a kan rikicin da ya barke tsakanin Dakta Isa Pantami, ministan sadarwa, da Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar NIDCOM, an gano cewa sakacin aiki ya hana a kiyaye faruwar rikicin.
SaharaReporters ta rawaito cewa sakacin tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari, wajen mika takardar korafin Dabiri-Erewa zuwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta taka rawa a rikicin na yanzu.
Pantami da Dabiri-Erewa sun samu sabani sakamakon takaddamar da ta shiga tsakaninsu a kan amfani da wani bangare na ginin hukumar NCC a matsayin ofishin sabuwar hukumar NDiCOM, mai kula da walwala da hakkokin 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare.
A wata wasika mai lamba: NIDC/CM/001/20/1 da Dabiri-Erewa ta aika zuwa ga shugaban kasa ta karkashin ofishin shugaban ma'aikatansa, ta bayyana yadda Pantami ya bayar da umarnin amfani da karfi domin hanasu shiga bangaren da su ke amfani da shi a matsayin ofis a ginin NCC.
NCC, hukumar kula da harkokin da su ka shafi kamfanonin sadarwa a kasa, ta na karkashin ma'aikatar sadarwa da Pantami ke shugabanta a matsayinsa na minista.
A cikin wasikar, wacce SaharaReporters ta wallafa a shafinta' Dabiri-Erewa ta yi kokarin sanar da shugaba Buhari abinda ya faru tsakanin hukumarta ta NIDCOM da ofishin ministan sadarwa.
Ta mika wasikar zuwa ga ofishin marigayi Abba Kyari domin gabatar da ita ga shugaban kasa, kamar yadda doka da tsarin aiki ya tanada.
Sai dai, wasikar, wacce Dabiri-Erewa ta rubuta tun ranar 13 ga watan Fabrairu, ba ta kai ga kan teburin shugaba Buhari ba har lokacin da Abba Kyari ya rasu.
DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 1000 - Buratai
A wani bangare na wasikar, Dabiri-Erewa ta rubuta cewa, "ya mai girma shugaban kasa, na rubuto wannan takarda zuwa gareka ne domin gaggauta sanar da kai korar karen da aka yi wa ma'aikatan hukumar NIDCOM daga ofishinsu da ke hawa na biyar a ginin hukumar NCC da ke Jabi, Abuja.
"ya mai girma, na rubuto domin sanar da kai wannan mummunan al'amari domin ka saka baki wajen warware wannan matsala.
"An hanamu shiga ofisoshinmu bisa umarnin ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami," a cewarta.
Rikicin na Pantami da Dabir-Erewa ya dauki sabon salo ranar Lahadi bayan sun fara cacar baki a dandalin sada zumunta na tuwita.
Da ya ke karyata zargin cewa an yi wa jami'an hukumar NIDCOM korar kare, Pantami ya ce, "wannan ba karamar karya ta ke yi ba. Tuni hukumar NCC ta karyata bayanan da ta bayar.
"Minista bai bawa wasu jami'an tsaro dauke da bindiga umarni ba. Ya kamata mu zama ma su gaskiya yayin bayar da bayani a kan kowanne al'amari. Ba ni da wani jami'in tsaro mai dauke da bindiga, kuma ban aika wasu ma su bindiga zuwa wurin ba."
Nan take Dabiri-Erewa ta mayar ma sa da martani da cewa, "bai kamata malamin addinin Musulunci ya ke karya ba. Ka yi min haka ne saboda ni mace ce, kuma da ma a bayyane ta ke cewa ba ka girmama mata.
"Amma ka taimaka ka saki kayanmu. Ofishin gwamnati ba wurin da za a dawwama ba ne."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng