Korona: Mutane 229 sun karu a Najeriya, jimilla ta haura 8,000
Hukumar NCDC ta fitar da sanarwar samun sabbin mutane 229 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar korona a fadin Najeriya a ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana tun bayan bullar annobar korona a Najeriya, jimillar ma su dauke da cutar korona a Najeriya ya haura dubu takwas.
Alkaluman NCDC na ranar Litinin sun nuna jerin jihohi a adadin mutanen da kowacce ta samu daga cikin jimillar ma su dauke da cutar kamar haka;
Lagos-90
Katsina-27
Imo-26
Kano-23
FCT-14
Plateau-12
Ogun-9
Delta-7
Borno-5
Rivers-5
Oyo-4
Gombe-3
Osun-2
Anambra-1
Bayelsa-1
A cewar NCDC, akwai jimillar mutum 8068 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar korona a Najeriya, ya zuwa karfe 11:34 na daren ranar Litinin.
An sallami jimillar mutane 2311 daga cibiyoyin killacewa daban-daban da ke fadin kasar nan bayan an tabbatar da cewa sun warke sarai.
Mutane 233 ne suka mutu sakamakon kamuwa da kwayar cutar korona, a cewar alkaluman hukumar NCDC na ranar 25 ga watan Mayu.
DUBA WANNAN: 'Yan N-Power sun tankawa minista Sadiya a kan biyan alawus, sun bukaci ta yi murabus
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta na kashe N4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar korona da aka kai cibiyar killace ma su cutar a jihar.
Rilwanu Mohammed, shugaban kula da cigaban harkokin lafiya a matakin farko, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi.
Ya ce gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ne ya bayar da umarnin a tabbatar cewa ana bawa masu cutar korona isashen abinci a cibiyar.
Wasu daga cikin ma su korona sun yi zanga - zanga domin nuna rashin jin dadinsu a kan yadda aka barsu kara zube a cibiyar killacewa.
Mohammed, shugaban bin diddigin ma su cutar korona a jihar, ya ce gwamna ya bayar da umarnin a tabbatar da cewa ma su cutar sun ji tamkar a gida su ke yayin da su ke cibiyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng