Sanwo-Olu: Babu maganar rage albashi saboda ka da jama’a su rasa aikin-yi
Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya na tabbatarwa mutanensa cewa annobar COVID-19 ba za ta sa ya taba albashin ma’aikatansa ba.
Gwamnan ya kuma yi magana game da halin da kanana da matsakaita kasuwanci za su iya shiga a Legas a daidai lokacin da Coronavirus ta ke ruguza karfin tattalin kasashe.
Mista Babajide Sanwo-Olu ya ce kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa za su shiga halin ha’ula’i idan ba a bude gari ba. Akwai miliyoyin mutanen da su ke amfana da SME a jihar.
Babajide Sanwo-Olu ya yi wannan jawabi ne a wani shiri da kungiyar First Securities Discount House ta gudanar ta kafar yanar gizo kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar.
Gwamnatin Legas ta kuma daga kafa ga ‘yan kasuwar da ke neman aron kudi daga hukumar LSETF mai kula da samar da aikin yi, domin rage radadin COVID-19 da ake ciki.
KU KARANTA: Gwamnati ta sassauta takunkumin da ta kakaba a kasuwannin Abuja
“Albashi abu guda ne da ba za mu iya tabawa ba. Harkokin wasanni, otel, zirga-zirga da sufurin jirgin sama sun girgiza sosai (da annobar cutar Coronvirus).” Inji gwamna Sanwo-Olu.
Mai girma gwamnan ya kara da cewa: “Wadannan harkoki, jiga-jigan karfin tattali ne. Mu na tunanin yadda za mu bi sannu a hankali wajen babbako da tattalin arziki da karfinsa.”
Saboda tausayin jama’an jihar, gwamnan ya bayyana yadda gwamnatin Legas ta hakura da irin abin da ta ke samu na kudin shiga domin gudun kamfanoni su sallami ma’aikatansu.
“Jihar Legas ta girgiza ta bangaren kiwon lafiya da tattalin arziki. Mun taba tattalin arzikinmu sosai, mun zaftare kusan 25%, wanda hakan abu ne mai yawa da ba za su so ba.” Inji sa.
Gwamnonin da su ka halarci wannan taro da aka yi ta yanar gizo sun hada da Mallam Nasir El-Rufa’i da Godwin Obaseki na jihohin Kaduna da Edo, inda su ka tofa albarkacin bakinsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa