Manufarmu su samu ilimin zamani ba tare da hanasu samin ilimin AlKur'ani ba - El-Rufa'i kan Almajirai
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ta gargadi iyayen da ke kai yaransu Almajirci da cewa za'a yi musu daurin shekaru biyu a gidan kaso.
El-Rufa'i ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda ya ziyarci wasu Almajirai 200 da aka kawo daga jihar Nasarawa kuma ake kula da su a kwalejin gwamnati dake Kurmin Mashi, Kaduna.
Gwamnan ya kara da cewa duk Malamin Allon da ya karbi yara zai fuskanci fushin hukuma inda za'a daureshi sannan a ci shi taran N100,000 ko N200,000 kan ko wani yaro.
Ya ce dukkan yara Almajirai da aka dawo da su daga wasu jihohi yan asalin jihar ne kuma gwamnati za ta basu daman cigaba a rayuwa.
El-Rufa'i ya nuna farin cikinsa bisa yadda yaga ana kula da Almajiran da kuma sauya rayuwarsu.
A cewarsa, jihar na da alhakin yin duk wani abun da ya kamata wajen baiwa Almajiran rana gobe mai kyau.
KU KARANTA: Masu Korona 8 kadai suka rage a jihar Zamfara, 65 sun warke - Matawalle
Yace: "Saboda haka, za mu cigaba da karban Almajirai yan asalin jihar Kaduna domin canza musu rayuwa, kula da shi tare da sanyasu a makarantu kusa da inda iyayensu ke da zama."
"Za mu cigaba da hakan har sai mun kawar da Almajirci daga jihar Kaduna, saboda ba hanyar samar da ilimi bane illa lalata rana goben yara."
"Babbar manufarmu ita ce su samu ilimin zamani ba tare da hanasu samin ilimin AlKur'ani ba."
"Zasu cigaba da karatun Al-Qur'ani amma karkashin iyayensu, ba karkashin wani wanda basu sani ba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng