Tsuntsu daga sama gasashshe: PDP ta fara zawarcin babban gwamna a jam’iyyar APC
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa a shirye take ta amshi gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki, don haka kofarsu a bude take a gare shi a duk lokacin da ya ji sha’awar shiga.
Daily Trust ta ruwaito Obaseki na APC na fama da rikicin gida a cikin jam’aiyyarsa a dalilin takun saka da ya shiga tsakaninsa da shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole.
KU KARANTA: Jagoran Super Eagles Ahmad Musa ya bayyana wanda ya lalata masa kwallo a Leicester
Oshiomhole tsohon maigidan Obaseki ne, kuma shi ya yi ruwa ya yi tsaki har Obaseki ya zama gwamna jahar Edo bayan tafiyarsa, shi ya mika masa mulki, don haka Oba ne ya gaji Adams.
Sai dai tun bayan kimanin shekaru biyu zuwa uku a karagar mulki aka fara samun sabani tsakanin mutanen biyu, har ta kai ga cacar baki tsakanin Oshimhole da Gwamna Obaseki.
Rikicin ne yasa ake ganin Oshiomhole zai yi kutun kutun don ganin APC bata tsayar da Obaseki ba, shi kuma Obaseki ba zai tsaya jiran a wulakanta shi ba zai koma PDP don samun takara.
A jawabinsa, shugaban PDP reshen yankin kudu maso kudancin Najeriya, Emmanuel Ogidi, ya ce kofarsu a bude take ga Obaseki, da ma duk wanda yake muradin komawa cikinta.
Ogidi ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa tawagar shuwagabannin PDP reshen jahar Edo a garin Bini a karkashin jagorancin Tony Aziegbemi inda yace:
“Idan Obaseki ya shigo, za mu amshe shi, ba zamu kori kowa daga jam’iyyarmu ba, kofofin mu a bude suke. Amma bani da wata masaniya game da shirinsa na shigowa jam’iyyarmu, idan har gwamnan ya ga haske, kuma ya shigo, muna masa maraba.
"Mu zai yi zaben fidda gwani, duk wanda ya ci shi ne dan takarar mu. Mun fara sayar da takardar takara, zamu gama a ranar Juma’a.” inji shi.
A nasa jawabin, shugaban PDP na jahar Edo yace abin da suke nema don samun nasara zaben gwamnan jahar dake karatowa kadai shi ne hadin kai.
Saboda a cewarsa jama’a sun nuna suna muradin canja APC bayan kwashe shekaru 11 tana mulkin jahar ba tare da tsinana musu komai ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com