Wani ya cinna wa 'yar uwarsa wuta ta mutu saboda ta yi wa mahaifiyarsu rashin kunya

Rundunar yan sandan jihar Legas ta kama wani Chima da ya bankawa yayarsa mai suna Victoria wuta a gidansu da ke CAC bus stop a Okokomaiko a unguwar Ojo.

Punch Metro ta ruwaito cewa yan uwan biyu suna taya mahaifiyarsu aiki ne a lokacin da ta ke girki nan rikici ya barke tsakanin Victoria da kanin ta Chima.

An gano cewa mahaifiyar tana yi wa jan kunnen Victoria ne a kan kwana a gidan mazaje tunda suka na gida amma sai cacan baki ya kaure tsakaninsu kuma Victoria ta fada wa mahaifiyarta magana mara dadi.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/881dfea5cce4ed10.png
Wani ya cinna wa 'yar uwarsa wuta saboda ta yi wa mahaifiyarsu rashin kunya. Hoto daga The Punch
Source: UGC

Rahoton ya cigaba da cewa munanan kalaman da Victoria ta fada wa mahaifiyarsu ne ya fusata Chima inda ya dako jarkar kalanzir ya buge ta da shi kuma kalanzir din ya zuba a jikinta da mahaifiyar.

DUBA WANNAN: Na kashe dan uwan na saboda mahaifin mu nuna masa kauna - Wanda ake zargi da kisa

Bayan haka sai wuta ta tashi a dakin girkin inda mahaifiyarsu da Victoria suka kone.

Domin ceto su, makwabta sun garzaya da su zuwa wani asibiti a Okokomaiko inda daga nan aka tura Victoria zuwa babban asibitin Igando. Amma Victoria ta mutu saboda munanan kunan da ta samu yayin da mahaifiyarsu ta samu sauki.

Chima ya yi kokarin tserewa bayan ya lura da abinda ya aikata amma matasan unguwar sun kama shi bayan sun hango hayaki na fitowa daga gidan kuma sun ji ihun wadanda wutar ta yi wa rauni.

Makwabtan sun kashe wutan sannan suka kima Chima hannun jamian yan sanda.

Da aka tuntube shi, Mai magana da yawun yan sandan jihar, Bala Elkana ya tabbatar da kama Chima inda ya kara da cewa Chima ya amsa cewa shi ne ya cinna wa yaruwarsa wuta saboda cin mutuncin mahaifiyarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng