Masu Korona 8 kadai suka rage a jihar Zamfara, 65 sun warke - Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammadu Bello Matawalle ya ce masu fama da cutar Coronavirus takwas kadai suka rage a jiharsa da aka killace a cibiyar killacewa.

Matawalle ya bayyana hakan jiya a wani taro a garin Maradun inda ya je more hutun bikin karamar Sallah (Eidul Fitr).

Gwamnan ya yabawa ma'aikatan kiwon lafiyan jihar bisa nasarar da suka samu wajen bibiyar wadanda suka kamu da cutar tare da jinyarsu.

Ya bayyana farin cikin cewa yanzu babu sabon mai dauke da cutar a jihar.

Yace: "Mun yi rashin mutane biyar sakamakon annobar amma wasu sun warke kuma daga baya aka sallamesu, suka koma wajen iyalansu cikin koshin lafiya."

"Wannan nasara ya samu ne bisa ga namijin kokarin ma'aikatan lafiyanmu, kokarin bin ka'idojin hana yaduwar cutar, da kuma hadin kan jama'ar jihar bisa bin dokoki."

"Ina son jaddada cewa COVID-19 gaskiya ce, har yanzu tana da hadari ga rayukan mutane. Saboda haka wajibi ne mu hada hannu wajen cigaba da bin ka'idojin hana yaduwar cutar a al'ummarmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng