Jagoran Super Eagles Ahmad Musa ya bayyana wanda ya lalata masa kwallo a Leicester
Jagoran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana dalilin da yasa bai cika samun isashshen lokacin da yake taka leda a tsohuwar kungiyarsa ta Leicester City ba.
Jaridar Sportinglife ta ruwaito Musa ya bayyana haka ne awata hira da yayi da Carol Tshabalala a dandalin sadarwar zamani na Instagram, inda yace Riyad Mahrez ne dalili.
KU KARANTA: Ji ka karu: Wasu halaye 10 marasa kyau dake janyo lalacewar kwakwalwar mutum
A watan Yulin shekarar 2016 ne Ahmed Musa ya tashi daga kungiyar CSKA Moscow na kasar Rasha ya koma Leicester ta kasar Ingila akan kudi pam miliyan 16.6.
Sai dai Musa bai samu daman taka leda yadda ya kamata ba, inda ya buga wasanni 22 ya ci kwallaye 2 kacal a kakar wasan shekarar.
Duk ba don komai ba sai don takwaransa Riyad Mahrez dan kasar Algeria na kungiyar, kuma yana taka rawa ainun a yadda ya kamata wajen samun nasarar kungiyar.
“Kafin Leicester City ta saye ni sun fada min cewa Riyad Mahrez zai tashi, da na san Mahrez ba zai tashi ba, da ban koma kungiyar ba, da na cigaba da zamana a CSKA Moscow.
“A lokacin da na je, muna da yan wasan gefe da dama a Leicester City, amma duk da haka na dan samu daman bugawa.” Inji shi.
Daga karshe dai Musa ya tattara inasa inasa ya koma CSKA Moscow a matsayin dan wasan aro a watan Janairun 2018, daga nan ya koma kungiyar Al Nassr ta kasar Saudi Arabia a shekarar.
A wani labarin kuma, dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Victor Osimhen ya rasa mahaifinsa a ranar Lahadi bayan jinya da yayi fama da ita.
Osimhen wanda ke taka leda a kungiyar Lille ta kasar Faransa da kansa ya sanar da rasuwar mahafin nasa a shafinsa na Twitter, dama dai tuni mahaifiyarsa ta mutu tun yan karami.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com