Gwamna Wike ya saki N450m na diyyar mamatan zaben 2019
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya saki kudi har naira miliyan 450 don rage radadin rikicin zaben 2019 da ya auku a yankin Ijaw
- Wike ya ce za a tura musu kudin ne ta asusun banki zuwa ranar Laraba
- Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya sadu da iyalan mamatan da kuma sarakunan gargajiya a dakin taro da ke Abonema a ranar Litinin
- Iyalan mamatan sun kai 37 wadanda suka rasa rayukansu yayin zaben kuma za a ba kowanne daga cikinsu diyyar naira miliyan 9
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya saki kudi har naira miliyan 450 don rage radadin rikicin zaben 2019 da ya auku a yankin Ijaw da ke Abonema, karamar hukumar Akuku-Toru ta jihar.
Gwamnan, wanda ya sadu da iyalan mamatan da kuma sarakunan gargajiya a dakin taro da ke Abonema a ranar Litinin, ya ce za a tura musu kudin ne ta asusun banki zuwa ranar Laraba.
Akwai alamun cewa, iyalan mamatan sun kai 37 wadanda suka rasa rayukansu yayin zaben kuma za a ba kowanne daga cikinsu diyyar naira miliyan 9.
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade ya amince da a cire wasu mutane da kungiyoyi da suka fada cikin masu karamin karfi daga cikin masu biyan haraji.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2020 yayin rantsar da kwamitin sassauci ga masu karamin karfi a jihar, Channels TV ta ruwaito.
Ayade yace duk wadanda ke kokarin samun na abinci basu cikin wadanda za su biya haraji a jiharsa.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigayi Abba Kyari yayi
Ayade ya fashe da kuka yayin da yake korafin yadda haraji ke takura wa masu karamin karfi a jihar.
Gwamnan ya ce bai taba sanin akwai jama'ar jihar da har yanzu suke rayuwa a gidan jinka ba.
Tsame masu karamin karfi daga biyan haraji tallafi ya shafi masu noma kadan, kasuwanci da masu ababen hawa na haya.
Ya ce masu siyar da abinci tare da duk wadanda ke gwagwarmayar samun na ci basu cikin wadanda za su biya haraji a jiharsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng