Ji ka karu: Wasu halaye 10 marasa kyau dake janyo lalacewar kwakwalwar mutum
Kwakwalwa, ita ce gaba muhimmanci a jikin dan Adam, amma mutane da dama suna wasa da ita, basu san muhimmancin kulawa da ita bar, har sai mai aukuwa ta auku.
Kwakwalwa na bukatar kulawa musamman don kyautata aikinta, don haka muka kawo muku wasu dabi’u guda 10 dake kawo ma kwakwalwa matsala kamar yadda The Nation ta ruwaito.
1- Rashin yin kalaci
Kwakwalwa na bukatar sinadaran abinci a wasu zababbun lokuta don yin aikinta yadda ya kamata, amma saboda sakaci da kuma yanayin rayuwa, sai kaga muna tsallake karin kumallo.
Rashin kalaci na kawo raguwar sinadarin siga a kwakwalwa da kuma karancin sinadarai masu amfani ga kwakwalwar, hakan na janyo kankancewar kwayoyin halittar kwakwalwa.
KU KARANTA: Bikin Sallah a Kaduna: Na yi wankan sallah amma babu wurin zuwa – Rahama Sadau ta koka
2- Rashin isashshen bacci
Takurai ma jiki da zai kai ga rashin samun isashshen bacci ba karamin matsala bane kwakwalwa, domin yana dakile muhimman ayyukan kwakwalwar.
Misali, mutum ya kan manta makullensa a gida, ko ya manta inda ya ajiye su, wannan na daga cikin matsalolin rashin isashshen bacci saboda yana kashe sinadaran halittar kwakwalwa.
Don haka masana suke shawartar mutum ya yi bacci na tsawon awanni 7 a rana.
3- Cin abinci da yawa
Kamar yadda karancin abinci ke kawo matsala ga kwakwalwa, haka cin abinci da yawa, yana narkar da kitsen kwakwalwa, ya sa jijiyoyin kai su yi kauri, don haka sai jini ya rage yawo.
Idan jini ya rage yawo a cikin kai, kwakwalwa na samun karancin jini, wanda hakan ke takaita aikin kwakwalwa.
4- Cin abinci mai siga
Halin da Adam ne cin siga, kuma yawan siga a jiki na sanya kwawalwa ta gaza sarrafa sinadaran abinci masu gina jiki, hakan na kawo rashin fahimta, gazawa wajen yin tunani.
5- Shan sigari/wiwi/shiha
Busa hayakin sigari ko wiwi da duk wani abu da ake busawa na kankantar da kwayoyin halittar kwakwalwa wanda hakan ke kai wag a mutuwa.
6- Rufe kai a lokacin bacci
Yayin da mutum ya rufe kansa lokacin da yake bacci, yana tara iskar da dan Adam fitarwa daga hancinsa watau Carbondioxide a cikin bargon, tare da rage adadin iskar da yake shaka Oxygen.
Nan da nan sai mutum ya fara wahalar shakar numfashi, daga nan sai kasala ya mamayeka.
7- Rashin motsa jiki
Ba sai an fadi muhimmancin motsa jiki ba, amma tabbas kwakwalwa na bukatar dan adam yana motsa jikinsa.
8- Shan giya
Yawan Kason giya a jikin dan Adam, yawan kwayoyin halittar kwakwalwa dake mutuwa, hakan kuma shi ke kankantar da girman kwakwalwar.
9- Sanya kida mai kara a kunne
Kida mai kara a kunne yana lalata tsokar kwakwalwa, saboda ita ke tantance sakon dake cikin kidar ko kuma duk abin da aka fada, don haka idan aka matsa mata sai ta lalace.
10- Gajiya
Hausawa suka ce rai dangin goro, hutu yake so, don haka wahalhalun neman kudi, na iyali da sauransu ka iya janyo ma mutum lalacewar kwakwalwarsa.
Wahala kan sa mutum shiga halin bakin ciki, rashin annushuwa, rashin walwala, rashin samun bacci, da sauransu, da zarar ka fara fuskantar wannan, Malam nemi wuri ka huta.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com