Ina da damar fitowa takarar shugaban kasa - Ministan Buhari

Ministan kwadago, Chris Ngige, ya yana da damar fitowa takarar kowacce kujerar siyasa a 2023 har da ta shugaban kasa da na gwamnan jihar Anambra a 2021 idan yana muradi.

Ministan ya sanar da hakan ne a karshen makon da ya gabata bayan mika tallafin rage radadi na abinci da suka kai kimanin N15 miliyan ga matalauta da masu bukata a yankin Alor.

Ya yi wannan zancen ne bayan rade-radin da ake yi na cewa zai fito takarar gwamnan jihar Anambra.

Ngige, wanda dan jam'iyyar APC ne, ya ce tallafin da ya bada bashi da alaka da wani burinsa na samun kujerar siyasa. Hakan yasa ya bai wa jama'a da ba 'yan jam'iyyar APC ba.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/629c96ac0015518c.jpg?imwidth=900
Ina da damar fitowa takarar shugaban kasa - Ministan Buhari Hoto: The Sun
Source: UGC

"Kowacce jam'iyya kake, matukar kana da bukata za a baka. Na fara da garinmu kuma zan taba karamar hukumar da kuma mazabarmu. Ina da burin kai wa majami'u don dole ne a bada tallafi gudun yunwa ta yi wa jama'a illa.

"Tabbas akwai rade-radin cewa ina hararar kujerar gwamnan jihar Anambra. An rubuto min wasika akan haka.

"Ni dan siyasa ne, suna da damar yi wannan hasashen. Amma kuma ina ganin ina da damar fitowa takara kowacce iri ce har da kuwa majalisar dattijai da kuma kujerar shugaban kasa," Ngige yace.

Amma kuma, ministan yace ya mayar da hankali ne wajen shawo kan kalubalen da ke tattare da kujerar da yake kai a yanzu fiye da wani burin siyasa.

"A halin yanzu, ina aikin kasata ne. Ni ne ministan kwadago. Kamar yadda kuka gani, akwai babban kalubale da ke gabanmu ballantana yadda tattalin arzikin kasar nan ke wani hali."

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigayi Abba Kyari yayi

Ya ce gidauniyarsa wacce ya kafa na kokarin tallafawa gidaje 1,000 tare da burin raba N5,000, shinkafa, indomie da sauransu ga mabukata.

A wani labarin kuma, mun ji cewa kansila dake wakiltar mazabar Galadama-Dangaladima a majalisar karamar hukumar Kaura-Namoda ta jahar Zamfara, Sagir Dansani ya ci dukan tsiya sa’annan aka masa tsirara.

Punch ta ruwaito kansilan ya bayyana haka ne daga gadon asibitin da yake jinya a garin Kaura Namoda, inda yace wasu miyagu ne suka dauke shi daga gidansa a ranar Asabar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng