Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigayi Abba Kyari yayi

Akwai alamu da ke nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sabon shugaban ma'aikatan fadarsa, Farfesa Ibrahim Agboola Gambari, ya soke nade-nade da kuma wasu ayyuka da marigayi Abba Kyari ya amince dasu ba tare da izininsa ba.

Duk da shugaban kasar bai bada wani dalili na wannan umarnin ba, amma rahotanni sun bayyana cewa a kalla marigayin ya amince da wasu al'amura 150 ba tare da sanin shugaban kasa Buhari ba.

Mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai na shugaban kasa, Femi Adesina ya tabbatar da hakan ga jaridar The Guardian ta sakon kar ta kwana amma kuma ya ki yin tsokaci a kan hakan.

Amma kuma babban mataimakin na musamman ga shugaban kasar a fannin yada labarai, Garba Shehu ya ki mayar da martanin sakon da aka tura masa.

Kyari ya rasu ne bayan kamuwa da muguwar cutar coronavirus da yayi.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/b4c370ffffa62fa3.jpg?imwidth=900
Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigayi Abba Kyari yayi Hoto: The Cable
Source: UGC

Aikin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ne yasa duk mai wannan mukamin ya zama mafi kusa kuma mafi rinjaye a ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Mutuwar Kyari ta zo ne a yayin da jama'a da dama ke kallonsa a matsayin na sahun gaba wajen juya kasar nan.

A lokacin da marigayi Kyari ya kamu da muguwar cutar coronavirus, jama'a da yawa da basu yarda da wanzuwar cutar coronavirus ba sun yada makamansu. Sun gani cewa cutar bata san matsayi, jinsi, kabila ko mulki ba.

Amma kuma yadda marigayin ya samu cutar ne ya bayyana irin karfin ikonsa duk da ba minista bane. Ya je daidaita al'amuran wutar lantarkin kasar nan ne a yayin da ya samo muguwar cutar.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace amarya da babbar kawarta a Katsina

Kamar yadda masu kusanci da fadar shugaban kasar suka bayyana, akwai hannun kyari a kusan komai da ke faruwa a kasar nan saboda iliminsa, hazaka da kuma gogewarsa.

A wani labarin na daban, Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar da ke kula da 'yan Najeriya da ke ci-rani a kasashen waje, NIDCOM, a ranar Lahadi sun yi musayar kalamai da Ministan Sadarwa a kan zargin korar maaikatanta daga ofishinsu.

A yayin da Dabiri-Erewa ta zargi Pantami ta rashin mutunta mata, ministan ya mayar da martani inda ya ce babu gaskiya ko kadan a cikin zargin da ta yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng