Sojin saman Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga 400 a Zamfara da Katsina - DHQ

Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta halaka sama da 'yan bindiga 200 a ruwan bama-baman da ta dinga musu a jihohin Zamfara da Katsina.

Shugaban sashen yada labarai na hedkwatar tsaro, John Enenche, a takardar da ya fitar ranar Lahadi, ya ce rundunar ta ci gaba da kokarin kakkabe 'yan bindiga a yankin.

Enenche ya ce an kashe 'yan bindiga a kalla 200 a sansanin 'yan bindiga da ke Mai Bai a karamar hukumar Jibia da kuma Kurmin Kura da ke Zurmi a Zamfara tsakanin ranar 22 zuwa 23 ga watan Mayu.

Ya ce an aiwatar da samamen ta jiragen yaki ne bayan tabbacin da suka samu na cewa wuraren biyu sun kasance maboyar 'yan bindigar kuma wurin adanar shanun sata.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, jiragen yakin sun tarwatsa maboyar 'yan bindigar tare da kashe shugabanni da mayakansu.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/e0e2271ad0460765.jpg?imwidth=900
Sojin saman Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga 400 a Zamfara da Katsina - DHQ Hoto: BellaNaija
Source: UGC

"Majiya mai karfi ta sirri ce ta tabbatar da halaka 'yan bindiga sama da 200 bayan harin da dakarun sojin saman suka kai wa masu.

"Shugaban rundunar sojin saman Najeriya ta jinjinawa rundunar Operation Hadarin Daji a kan nuna kwarewarsu da suka yi. Ya umarcesu da su mayar sa hankali wajen kakkabe ragowar 'yan bindigar.

"Shugaban rundunar sojin saman Najeriya ya bada umarnin kara tura kayan aiki jihohin Kaduna, Niger, Nasarawa da Kogi don dakile duk wani harin 'yan bindiga," yace.

KU KARANTA KUMA: Yansanda sun dirka ma matashi bindiga yayin da yake yin alwala a kofar gida

A gefe guda mun ji cewa a kalla 'yan bindiga 50 ne suka tsinkayi garin Yankara da ke karkashin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a ranar Asabar da ta gabata.

'Yan bindigar sun yi awon gaba da wata amarya tare da babbar kawarta ana saura sa'o'i 48 daurin aure, SaharaReporters ta ruwaito.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce 'yan bindigar sun tsinkayi kauyen wurin karfe 11:30 na dare inda suka yi awon gaba da Shanu.

Ya ce sun isa kauyen a kan babura kuma da dare a lokacin da mutane da yawa suke bacci. Sun isa gidan amarya tare da bukatar a miko ta da babbar kawarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng