Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace amarya da babbar kawarta a Katsina

A kalla 'yan bindiga 50 ne suka tsinkayi garin Yankara da ke karkashin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a ranar Asabar da ta gabata.

'Yan bindigar sun yi awon gaba da wata amarya tare da babbar kawarta ana saura sa'o'i 48 daurin aure, SaharaReporters ta ruwaito.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce 'yan bindigar sun tsinkayi kauyen wurin karfe 11:30 na dare inda suka yi awon gaba da Shanu.

Ya ce sun isa kauyen a kan babura kuma da dare a lokacin da mutane da yawa suke bacci. Sun isa gidan amarya tare da bukatar a miko ta da babbar kawarta.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/ec04678413f55a3b.jpg
Tirkashi: 'Yan bindiga sun sace amarya da babbar kawarta a Katsina Hoto: Channels Television
Source: UGC

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina dai yace cutar coronavirus ba matasala bace a jihar, matasalar 'yan bindiga ta sha gaban annobar.

KU KARANTAKUMA: Mutanen gari sun babbaka mutane 12 da suke zarginsu da maita a Cross Rivers

A cikin wata daya tak da ya gabata, 'yan bindiga sun halaka a kalla mutum 100 a jihar Katsina.

A wani laari na daban, wani matashi mai suna Sadiq Abubakar Ibrahim ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali bayan Yansandan babban birnin tarayya Abuja sun harbe shi yayin da yake yin alwala a kofar gida.

Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Mayu a gidansu dake Gwarimpa yayin da Yansandan sanye da kayan gida dauke da bindigogi suka far ma gidan nasu.

Sai dai Yansandan sun ce suna bin sawun wani mai garkuwa ne a unguwar a lokacin da suka ga Abubakar ya tsere daga ganinsu, don haka suka dauka shi ne barawon, sai suka bindige shi.

Amma a bangarensa, Abubakar da Iyayensa sun bayyana cewa sun dauka Yansandan yan fashi da makami ne ko kuma masu garkuwa da mutane, don haka suka razana, kowa ya tsere.

Kwamandan Yansandan ya bayyana cewa jamiā€™ansa sun ce masa ba su harbi Sadiq ba,yankewa yayi da wayar karfe dake kan katangar gidan makwabcinsu da yayi kokarin tsallakawa.

A cewar Fatima da kyar Yansanda suka basu Sadiq don a kai shi asibiti duk da cewa yana da zubar da jini, kuma basu sake duba shi ba, balle su biya kudin asibitinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng