Yansanda sun dirka ma matashi bindiga yayin da yake yin alwala a kofar gida
Wani matashi mai suna Sadiq Abubakar Ibrahim ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali bayan Yansandan babban birnin tarayya Abuja sun harbe shi yayin da yake yin alwala a kofar gida.
Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Mayu a gidansu dake Gwarimpa yayin da Yansandan sanye da kayan gida dauke da bindigogi suka far ma gidan nasu.
KU KARANTA: Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Atiku Abubakar
Sai dai Yansandan sun ce suna bin sawun wani mai garkuwa ne a unguwar a lokacin da suka ga Abubakar ya tsere daga ganinsu, don haka suka dauka shi ne barawon, sai suka bindige shi.
Amma a bangarensa, Abubakar da Iyayensa sun bayyana cewa sun dauka Yansandan yan fashi da makami ne ko kuma masu garkuwa da mutane, don haka suka razana, kowa ya tsere.
Wata yar uwar Sadiq, Fatima Babashehu ta bayyana cewa: “Babar Sadiq na cikin gida tana aiki sai kawai ta ji mutane suna dira gidanta ta Katanga a gude, don haka ita ma ta tsere zuwa kicin ta garkame kofa.
“Sai suka fara dukan kofar suka bukaci ta bude, bayan ta bude suka fito da kowa dake gidan, suka fara bincikensu da dakunansu a nan ne suka ci karo da Sadiq yana alwala a gefen gidan, ganinsu ke da wuya sai ya razana ya tsere ya dauka yan bindiga ne.
“Har ya yi kokarin tsallaka Katanga, a daidai lokacin nan ne suka bindige shi a hannu, sun cigaba da bin sa har sai da suka kamo shi a gidan makwabta, inda suka kama makwabcin da yaransa biyu, sa’annan suka yi awon gaba da kowa da kowa.
“Babu wanda ya san inda suka fito, daga bisani bayan mun yi ta buga waya ne muka gane ashe Yansanda ne, daga nan muka wuce ofishin Yansanda dake Guzate, a nan ne aka fada mana wai suna bin sawun wani barawon mutane ne, kuma na’urar bincike ta nuna musu a gidanmu yake.” Inji ta.
Kwamandan Yansandan ya bayyana cewa jami’ansa sun ce masa ba su harbi Sadiq ba,yankewa yayi da wayar karfe dake kan katangar gidan makwabcinsu da yayi kokarin tsallakawa.
A cewar Fatima da kyar Yansanda suka basu Sadiq don a kai shi asibiti duk da cewa yana da zubar da jini, kuma basu sake duba shi ba, balle su biya kudin asibitinsa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com