Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun saka dokar hana fita na kwana 3 a Bayelsa
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bayelsa ta saka dokar hana fita daga safe zuwa dare na tsawon kwanaki uku.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Uche Anozia ne ya bayar da sanarwar a ranar Juma'a kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Hakan ba zai rasa nasaba ba da barkewar rikici a jihar bayan da kotun koli ta soke zaben Lyon na jam'iyyar APC kuma ta umurci hukumar zabe ta mika takardan shaidan nasarar cin zabe ga dan takarar PDP, Diri.
An soke zaben Lyon ne bayan da kotun kolin ta ce abokin takararsa ya gabatarwa INEC ta takardun bogi.
DUBA WANNAN: Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48
Fusatattun masu zanga-zanga da ake kyautata zaton yan jam'iyyar APC ne sun kai hari gidan zababben gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, kan nasarar da kotun koli ta bashi bayan sallamar David Lyon na APC.
Masu zanga-zangan sun lalata dukiyoyin jiga-jigan 'yan jam'iyyar PDP a babbar birnin jihar Yenegoa.
Sun fasa gilasan motocin da ke ajiye cikin gida bayan balla kofofi da tagogin da ke ciki.
Kazalika sun kai farmaki dakin karatun dan majalisar wakila mai wakiltar Yenegoa da Kolokuma/Opokuma, Steve Azaiki, sakatariyar PDP da kuma gidan rediyon jihar.
Mun kawo muku rahoton cewa Zanga-zanga ya barke a sassan Yenegoa, babbar birnin jihar Bayelsa kan shari'ar kotun kolin tarayya da ta hana rantsar da Cif David Lyon, a matsayin gwamnan jihar.
Duban mata sun tare manyan hanyoyin jihar domin inda suka lashi takobin cewa babu wanda za'a rantsar gwamnan jihar Bayelsa yau.
Sai dai duk da hakan hukumar zabe ta INEC ta mika wa Diri takardan shaidan lashe zaben.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng