Likitoci dubu 1 da 716 sun kamu da cutar Corona a China
by Azima Bashir Aminu, Bashir Ibrahim IdrisYayin da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 ke cigaba da hallaka jama’a a kasar China, rahotanni sun ce ma’aikatan lafiya dubu 1 da 716 suka kamu da cutar, daga cikin ma’aikata 80,000 da ke kula da masu dauke da cutar.
Hukumomin kasar China sun ce daga cikin mutane kusan 1,400 da suka sheka lahira, 6 ma’aikan lafiya ne, wadanda ke cikin jami’an da ke kula da wadanda suka kamu da cutar 1,716 da suma yanzu haka ake kula da lafiyar su.
Gwamnatin China ta ce yanzu haka ma’aikatan lafiya 80,000 ke aiki ba dare, ba rana wajen kula da masu fama da cutar, wadda aka ruwaito cewar ta shiga wasu kasashe kusan 30 na duniya.
A yankin Hubei inda annobar cutar ta fi tsananta, hukumomi sun ce an samu karin mutuwar mutane 116, yayin da wasu sama da 4,800 suka kamu da ita.
Michael Ryan na hukumar lafiya ta duniya ya ce, yawan adadin mutanen da aka samu ranar laraba, bai sauya yadda cutar ke yaduwa a cikin jama’a ba.
Yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke yabawa China dangane da rawar da ta ke takawa wajen shawo kan annobar, kasar Amurka na zargin China da rufa rufa dangane da lamarin.