http://s.rfi.fr/media/display/5d0c0b48-4f3f-11ea-b919-005056bf87d6/w:1024/p:16x9/2017-09-19t142159z_372065605_rc190dc9acc0_rtrmadp_3_usa-trump-weapons.jpg
Hada-hadar cinikayyar makamai.REUTERS/John Sommers II/File Photo

An samu karuwar cinikayyar makamai a duniya- Rahoto

by

Wani rahoto kan hada-hadar makamai a duniya ya nuna yadda aka samu karuwar cinikayyar makaman da akalla kashi 4 cikin shekaru 10 da suka gabata, inda kasashen Amurka da China ke matsayin kan gaba wajen kara yawan kudaden da suke kashewa da nufin mallakar makamai.

Rahoton wanda cibiyar bincike kan dabarun siyasar kasashen duniya ta IISS ta fitar yau Juma’a ta nuna cewa shirin zamanantar da harkokin tsaro na Beijing da ya kunshi samar da sabbin makamai masu linzami da makaman kakkabo makamai baya ga shirin Washington na fadada harkokin tsaro sun taimaka matuka wajen karuwar hada-hadar cinikayyar makamai a duniya.

Cibiyar IISS ta ce kasashen Amurka da China sun kara kasafin bangaren makamansu da kashi 6.6 yayinda Rasha ta karfafa bangaren makaman da kashi 4.2, batun da cibiyar ta bayyana da abin tayar da hankali.

Cikin rahoton shekara-shekara da cibiyar kan fitar game da harkokin tsraon kasashe, ta ce daga 2018 zuwa 2019 Amurka ta kashe kudin da ya kai dala biliyan 53 da rabi wajen makamai, wanda ke neman kere ilahirin kasafin bangaren tsaron Birtaniya.

Sai dai duk da wannan hauhawar cinikayyar ta Makamai, rahoton ya ce a nahiyar Turai ba hakan abin yak e ba, inda IISS ke cewa an samu koma baya a kudaden da kasashen nahiyar ke kashewa bangaren makamai tun daga 2008 gabanin shaguben Donald Trump na Amurka a baya-bayan nan da ke bayyana yadda tsaron nahiyar ta ta’allaka ga kudaden da Amurka ke samarwa kungiyar tsaro ta NATO.

A baya-bayan nan dai Trump ya matsanantawa kasashen Turai wajen ganin sun kara kasafin kudin da suke yiwa bangaren tsaro don tafiya kafada-da-kafada da Amurka.