http://s.rfi.fr/media/display/72ca5fe4-4f20-11ea-a690-005056bfd1d9/w:1024/p:16x9/2019-02-20t153817z_1620374022_rc1c867f5670_rtrmadp_3_nigeria-election_0.jpg
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Farfesa Yakubu Mahmood.REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumar zabe ta bayyana Diri a matsayin zababben gwamnan Bayelsa

by

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana Sanata Duoye Diri, dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa a matsayin wanda ya zama zababben gwamnan jihar samakamon hukuncin kotun koli da ya soke nasarar Jam’iyyar APC.

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya shaidawa manema labarai cewar, sun samu takardun kotu dangane da hukuncin jiya, kuma bayan nazari a kai, sun amince da cewar Sanata Diri na Jam’iyyar PDP da ya zo na biyu a zaben da akayi aJihar, shine zababben Gwamna.

Farfesa Yakubu yace za’a mikawa Sanata Diri da mataimakin sa takardar shaidar nasarar da suka samu domin ganin an rantsar da su kan mukaman su.

Idan dai ba’a manta ba, jiya ne kotun kolin Najeriya ta soke zaben da aka yiwa David Lyon na Jam’iyyar APC saboda abinda kotu ta gano na gabatar da bayanan karya da mataimakin sa ya yiwa hukumar zabe.

Tuni Jam’iyyar APC tayi watsi da hukuncin ta hannun shugaban ta Adams Oshiomhole, yayin da PDP ta bayyana farin cikin ta da hukuncin ta hannun shugaban ta Uche Secondus da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.