Yanzu Yanzu: An hana Diri shiga hedkwatar INEC

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an hana dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jahar Bayelsa da aka gudanar a kwanaki, Diri Douye shiga hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), inda ya je karban takardar shaidar cin zabe.

Jami’an tsaro wadanda suka yiwa mashigin hedkwatar kawanya ne suka hana diri wanda ya isa wajen da misalin karfe 11:15 shiga wajen.

Da farko dai mun ji cewa Diri Douye da wasu masu ruwa da tsaki sun dura zuwa harabar hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), inda suke nemi a basu takardar shaidar cin zabe.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu da wasu kwamishinonin hukumar na kasa suka yi ganawar sirri a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Koda dai babu wani jawabi daga mahukunta kan dalilin ganawar nasu, jaridar The Nation ta tattaro cewa ana ganawar ne domin yin nazarin hukuncin kotun koli wacce ta tsige zababben gwamnan Bayelsa, David Lyon.

An kuma tattaro cewa shugaban hukumar zai yiwa manema labarai jawabi

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/f5e4d7173954c33d_w.jpg
Yanzu Yanzu: Shugabannin INEC sun shiga labule kan hukuncin kotun koli a Bayelsa
Source: Original

Kwamishinan INEC na kasa kuma Shugaban kwamitin bayanai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye a ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu ya ce hukumar na nazarin hukuncin.

A wani labarin kuma mun ji cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta soki hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin zababben gwamnan jahar Bayelsa.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyar na iya shigar da bukatar sake duba ga hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin gwamnan jahar Bayelsa.

Da ya ke martani kan hukuncin kotun kolin, Oshiomhole ya ce tuni jam’iyyar ta tuntubi lauyoyinta kan matakin da ta ke shirin dauka don tabbatar da ganin an dawo wa da Lyon hakkinsa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Bauchi ya taya Douye Diri murna kan hukucin kotun koli a zaben gwamnan Bayelsa

Babbar kotun ta tsige Mista Lyon a ranar Alhamis, 13 ya watan Fabrairu kan hujjar cewa mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatar da satifiket na bogi ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng