Gwamna El-Rufai ya ware naira biliyan 4.7 don baiwa daliban Kaduna tallafi
Gwamnatin jahar Kaduna ta ware kimanin naira biliyan 4.7 domin daukan nauyin daliban jahar Kaduna dake karatu a kasashen waje tare da baiwa wadanda suke karatu a gida tallafi, kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN, ta ruwaito shugaban hukumar Hassan Rilwan ne ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labaru a ranar Alhamis, 13 ga watan Feburairu, a garin Kaduna.
KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama manyan daraktoci da satar naira biliyan 700
Malam Hassan ya bayyana cewa sun biya kudin tallafi ga dalibai 4,400 a cikin dalibai 7, 598, sa’annan ya kara da cewa sun tura dalibai karatu zuwa kasar Amurka, Birtaniya, Australia, Jamus da kuma Cuba.
“Daga cikin daliban akwai Abba Dauda Maitala wanda ya samu tallafin naira miliyan 15 don yin karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar tsaro na yanar gizo a jami’ar Northumbria dake garin Newcastle, Birtaniya.
“Ahmad Musa da ya samu tallafin karatu na naira miliyan 28.8 don yin karatun digiri na uku a jami’ar Potsdam dake Jamus, Sharif Ahmad Habibu shi kuma ya samu tallafin naira miliyan 9.8 don yin digiri na uku a jami’ar Swinburne dake Australia.” Inji shi.
Hassan ya bayyana cewa a kasafin kudin shekarar 2020 gwamnatin Kaduna ta ware naira biliyan 4.7 don tallafin karatu, wanda yace hakan ya nuna muhimmancin da Gwamna El-Rufai ya baiwa ilimi.
“Akwai naira biliyan 2 da aka ware don bayar da bashi ga masu son yin karatu, jama’an jahar Kaduna zasu iya neman har zuwa naira miliyan 5 a matsayin bashi don amfaninsu ko kuma karatun yaransu a ciki da wajen kasar nan, sharadi kawai shi ne su kawo mutane biyu da zasu tsaya musu, mutanen su kasance ma’aikatan gwamnatin tarayya.” Inji shi.
Daga karshe Hassan yace kowa na da damar samun wannan tallafi matukar mazaunin jahar Kaduna ne, kuma sun kawo nagartaccen tsarin zabo daliban da suka cancanta ba tare da nuna sanayya ko son kai ba, haka zalika suna biyan kudin a lokacin daya kamata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa