Yanzu-yanzu: INEC ta baiwa Duoye Diri na PDP shahadar nasarar zaben gwamnan Bayelsa

Hukumar gudanar da zabe ta kasa ta alanta Sanata Duoye Diri na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa kuma zata bashi shahadar nasarar zaben gwamnan Bayelsa.

A yanzu haka, ana bikin gabatar masa da shahadar nasarar zaben

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/014931371b475460.jpg
Yanzu-yanzu: INEC ta baiwa Duoye Diri na PDP shahadar nasarar zaben gwamnan Bayelsa
Source: Facebook

Zanga-zanga ya barke a sassan Yenegoa, babbar birnin jihar Bayelsa kan shari'ar kotun kolin tarayya da ta hana rantsar da Cif David Lyon, a matsayin gwamnan jihar.

Dubunnan mata sun tare manyan hanyoyin jihar domin inda suka lashi takobin cewa babu wanda za'a rantsar gwamnan jihar Bayelsa yau.

Ana saura awanni kasa da 24 da rantsar da sabon gwamna, kotun koli a ranar Alhamis ta fitittiki David Lyon a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa tare da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo bayan sun lashe zaben 16 ga Nuwamba 2019.

Alkali Ejembi Eko, wanda ya karanto da shari'ar ya yi amfani da shari'ar babbar kotun tarayya dake Abuja da ta hana Degi-Eremiwoyo takara a zaben gwamnan.

Kotun kolin ta tabbatar da shari'ar karamar kotun cewa zababben mataimakin gwamnan ya aikata laifi wajen gabatar da kwalin bogi ga hukumar INEC.

Kwamitin Alkalan kotun koli kan karar karkashin jagorancin, Mary Odili, sun yi ittifakin cewa mutum bai cancanci takara a zabe ba muddin ya gabatar da takardun boge domin zaben.

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta shigar da kara kotu kan zargin gabatar da takardun boge da take yiwa dan takarar kujerar mataimakin gwamnan APC, Degi-Eremienyo.

Sun tuhumceshi da gabatar da sunayen daban-daban guda biyar matsayin sunayensa cikin kwalayen karatunsa.

PDP ta ce sunan zababben mataimakin gwamnan dake cikin kwlain karatun firamarensa ya banbanta da na sakandare hakazalika na jami'a.

Ga jerin yadda sunayensa sukea kwalayen:

Kwalin karatun Firamare - Degi Biobara

Kwalin karatun Firamare - Adegi Biobarakumo

Kwalin karatun Jami'a- Degi Biobarakuma

Kwalin karatun Jami'a MBA - Degi Biobarakuma Wangaha

Sunansa a zaben 2019 - Degi-Eremienyo Biobarakuma

Wannan shine dalilin da ya sa kotun koli ta fitittiki zababben gwamnan da mataimakinsa saboda tikitin da sukayi takara daya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng