NFF ta baiwa Yobo mukamin mataimakin kocin Najeriya
by Nura Ado SuleimanHukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta nada tsohon dan wasan Super Eagles mai tsaron baya Joseph Yobo, a matsayin mataimakin kocin tawagar kwallon kafar kasar Gernot Rohr.
A baya dai Imama Amapakabo ne ke rike da matsayin na mataimakin kocin na Najeriya.
Bayan wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 a 1999 ne Yobo ya soma bugawa babbar tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles, wanda ya kasance cikin ‘yan wasan da suka fafata wasannin gasar cin kofin nahiyar Afrika guda 6, a tsakanin shekarun 2002 zuwa 2013, lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar ta Afrika.
A Turai kuwa Joseph Yobo ya kafa tarihin zama dan Afrika na farko ya zama kaftin din kungiyar Everton dake Ingila, kungiyar da ya bugawa wasanni 250, tare da taimaka musu samun damar shiga gasar cin kofin zakarun Turai a 2009.