Hukuncin kotun koli kan Bayelsa hatsari ne ga damokradiyyar Najeriya - APC
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta soki hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin zababben gwamnan jahar Bayelsa.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyar na iya shigar da bukatar sake duba ga hukuncin kotun koli wacce ta tsige dan takararta, David Lyon, a matsayin gwamnan jahar Bayelsa.
Da ya ke martani kan hukuncin kotun kolin, Oshiomhole ya ce tuni jam’iyyar ta tuntubi lauyoyinta kan matakin da ta ke shirin dauka don tabbatar da ganin an dawo wa da Lyon hakkinsa.
Babbar kotun ta tsige Mista Lyon a ranar Alhamis, 13 ya watan Fabrairu kan hujjar cewa mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatar da satifiket na bogi ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a yayin zaben.
Douye Diri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne ya zo na biyu a zaben sannan ya samu kaso 25 cikin dari na kuri’u a biyar daga cikin kananan hukumomin Bayelsa guda takwas sannan ana sanya ran shi za a bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 16 ga watan Nuwamba.
Sai dai kuma, shugaban jam'iyya mai mulki na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce "hukuncin baya tare da adalci" kuma tana a kan fasaha ne kawai wanda ya ke "hatsari ga damokradiyya.
"A inda aka daura adalci da damokradiyya kan teburin fasaha, yana nuna hatsari ga damokradiyya. Babu wansa ya ta da zantukan ko David Lyon da abokin takararsa sun lashe mafi rinjayen mutane," in ji a sakatariyar jam'iyyar a yammacin ranar Alhamis.
Mista Oshiomhole ya ce gaba da cewa: “Dan takarar PDP bai da kaso daya cikin hudu na dukkanin amintattun kuri’un da aka kada a zaben a kaso biyu cikin uku na kananan hukumomi takwas da ke jahar Bayelsa.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar Musulunci ta yi Allah wadai da ka'idojin daukan ma'aikatan Amotekun
A wani labarin kuma, mun ji cewa zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon wanda kotun koli ta tube a yau Alhamis ya bayyana cewa tun kafin a rantsar da shi ne aka bashi gwarzon gwamnoni na shekarar 2019. Gwamnan ya bayyana cewa an bashi wannan karramawar ne tun kafin a rantsar da shi.
Tubabben gwamnan ya wallafa wannan bidiyon ne a shafinsa na tuwita. Duk da dai har a halin yanzu ba a san daga inda kyautar karamcin ta fito ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Amma a yayin kwatanta karramawar, ya ce “abin na Ubangiji ne”. Lyon ya kara da cewa bai saba karbar ire-iren wadannan kyautukan ba amma ya karba na wannan karon ne saboda ku.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng