http://s.rfi.fr/media/display/258dd898-1067-11ea-8639-005056bf7c53/w:1024/p:16x9/d2c88819aa3142b2a825cfdafb214a50.jpg
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.AFP

NDF ta bukaci Buhari ya kafa dokar ta baci a Borno

by

Kungiyar National Democratic Front NDF mai fafutukar tabbatar da shugabanci na gari da tsarin dimokaradiyya, ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a Borno, biyo bayan sabbin hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a sassan jihar.

Kungiyar da babban ofishinta ke Philippines ta kuma bukaci Buhari ya dakatar da baiwa kananan hukumomin jihar ta Borno kudaden gudanarwa, abinda tace yana taka rawa wajen sanya marasa zaman lafiyar dake amfana da kudaden yiwa kokarin murkushe barazanar tsaron zagon kasa.

A larabar da ta gabata, 12 ga Fabarairu, dakarun Najeriya suka gwabza fada da mayakan Boko Haram da suka afkawa wasu yankunan wajen birnin Maiduguri.

Kungiyar ta Boko Haram ta kai farmakin ne jim kadan bayan kammala ziyarar da shugaban Najeriyar Muhammadu ya kai jihar ta Borno, domin jajanta kisan gillar da masu tada kayar bayan suka yiwa akalla mutane 30 Auno dake wajen birnin Maiduguri.

Ana kyautata zaton cewar mayakan da ke biyayya ga Abubakar Shekau ne suka kai kazamin harin na ranar Lahadin da ta gabata, kan fasinjojin da suka kwana a garin Auno, mai nisan kilomita 25 daga garin Maiduguri, sakamakon rufe hanyar shiga birnin da sojoji suka yi.

Daga cikin wadanda abin ya rutsa da su har da wata mata mai shayar da jariri, wadda wuta ta kone tare da jaririnta, sakamakon banka ma wata tankar dakon man fetur wuta da maharan suka yi.

Maharan sun kuma sace mutane da dama yayin farmakin.