Annobar COVID-19 ka iya tafka barna fiye da 'yan ta'adda - WHO
by Nura Ado SuleimanHukumomin Lafiyar China sun ce an samu karin mutane 121 da annobar murar mashako ta COVID-19 ta halaka a China, kuma 116 daga cikin mamatan sun fito ne daga Lardin Hubei kadai, inda annobar ta samo asali.
Yanzu haka dai annobar cutar ta COVID-19 dake kassara hanyar numfashin dan adam ta halaka jimillar mutane dubu 1 da 488 a kasar ta China.
Kididdigar baya bayan nan da jami’an lafiya a kasar suka fitar kuma ta nuna cewar, mutane dubu 51 da 986 ne suka kamu da murar mashakon ta COVID-19 a Lardin Hubei kadai, tun bayan bullarta a Wuhan babban birnin lardin.
A fadin kasarta China kuwa sabuwar kididdigar ta ce kusan mutane dubu 65 annobar ta shafa, bayan gano karin mutane dubu 5 da 90 da suka kamu.
Kawo yanzu dai annobar murar ta COVID-19 ta bazu zuwa akalla kasashe 25, inda ta halaka mutane 3, a Hong Kong, Philippines da kuma Japan.
A baya bayan nan shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus yayi gargadin cewar, cutar ka iya tafka barna sama da ayyukan ‘yan ta’adda.