Babbar magana: Na yadda akwai Allah, amma zancen wuta da aljannah kanzon kurege ne a wajena - Efia Odo
- A yayin da kowa yake kokarin ya ga ya cika da imani, kuma ya dage yake aiki tukuru domin samun hanyar shiga Aljannah da kuma nesanta daga wutar lahira
- Sai gashi fitacciyar jaruma 'yar kasar Ghana Efia Odo, ta fito ta karyata zancen cewa akwai wuta da aljannah
- Jarumar ta ce tabbas ta yadda akwai Allah, amma ita zancen wuta da aljannah duk kanzon kurege ne a wajen ta
Fitacciyar jaruma ‘yar kasar Ghana, Efia Odo ta karyata imanin da Kiristoci suke da shi na cewa akwai wuta da aljannah.
Kasar Ghana dai akasari kasa ce ta Kiristoci, inda ‘yan kasar da yawa suka yadda cewa akwai wuta da aljannah, kuma suke muradin idan sun mutu za su shiga aljannah yayin da suke kuma addu’ar ganin makiyansu a wuta.
Tsohuwar al'adace a kasar Ghana mutane su dinga yiwa makiyansu fatan Allah ya sanya su a cikin wutar jahannama, duku kuwa da hakan ba wai hali ne mai kyau ba.
Koma dai yane dai jarumar ta fito a shafunta na Twitter ta karyata wannan magana da Qur'ani da kuma littafin Bible suka zo da su, inda ta ce ita sam ba ta yadda da wannan magana ba, kuma ta dauke ta a matsayin kanzon kurege.
KU KARANTA: Tirkashi: Wani mutumi da ya mutu ya tashi yayin da ake kokarin sanya shi a kabari
A cewar ta, ita ta yadda akwai Allah, amma ba ta yadda akwai wuta da aljannah ba.
Jarumar fim din tayi rubutu a shafinta na Twitter kamar haka: “Na yadda akwai Allah. Amma wuta da aljannah ba wurare bane a wajena. Babu wanda ya taba zuwa can ya gani. Idan har kayi rayuwa ta gaskiya, idan ka mutu ranka zai kwanta cikin jin dadi. Idan kuma kayi rayuwar da ta sabawa haka ranka zai kwanta cikin tashin hankali.”
To wannan dai na zuwa ne a lokacin da kowanne mutum yake dagewa da aiki tukuru domin ganin ya samu ya dace da shiga Aljannah ya kuma nesanta kanshi daga azabar wuta.
Wannan magana da jarumar tayi ta jawo kace-nace matuka a shafinta na Twitter, inda wasu ke ganin cewa kamar imaninta bai cika ba, indai har za tayi wannan furuci, domin kuwa duk wani Musulmi da Kirista da ya yadda da Allah ya tabbata da cewa akwai azabar wuta da aljannah.
Haka kuma mun kawo labarin wani fitaccen dan siyasa dan asalin kasar Netherlands da ya karbi addinin Musulunci.
Mutumin wanda yake dan majalisa ne, mai suna Joram Van Klaveren, a shekarun da suka wuce babu wanda ya kai shi kyamar addinin Musulunci.
Kiyayyar Joram a wancan lokacin har ta kai ga ya kira littafin Al-Qur'ani mia girma da cewa guba ne. Sai dai abin mamaki shine, Joram ya Musulunta ne a lokacin da yake rubuta wani littafi na nuna kiyayya ga addinin Musulunci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng