Masha Allah: Sarauniyar kyau ta duniya 'yar kasar Czech Republic ta Musulunta

- Tsohuwar budurwar da ta lashe gasar sarauniyar kyau ta duniya 'yar asalin kasar Czech Republic ta karbi addinin Musulunci

- Budurwar mai suna Marketa Korinkova ta Musulunta ta kuma canja sunan ta zuwa Maryam

- Yanzu haka ta bar kasar Czech Republic ta koma kasar Dubai domin ta yi ibada yadda ya kamata

Tsohuwar sarauniyar kyau ta kasar Czech Republic, Marketa Korinkova ta Musulunta inda ta canja sunan ta zuwa Maryam.

Ta ce yanzu haka ta karbi addinin Musulunci kuma ta bar kasarta ta haihuwa ta koma kasar Dubai da zama domin gabatar da addininta a tsinake.

Ta ce matsayin da addinin Musulunci ya bawa mace shine ya jawo hankalinta ta shigo addinin, ta kara da cewa ta shafe shekaru uku ta so ta dawo addinin Musulunci, amma sai bayan ta koma Dubai ta bayar da sanarwar cewa ta Musulunta.

A wani rahoto da jaridar Al Quds-al-Arabi ta fitar ta bayyana cewa, musuluntar Marketa ta yi sanadiyyar da masoyanta da dama suka biyo ta cikin addinin Musulunci.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/782ae0eab62240b9.jpg
Masha Allah: Sarauniyar kyau ta duniya 'yar kasar Czech Republic ta Musulunta
Source: Facebook

A wata gasar kyau da aka gabatar a kasar Italy, Marketa ce ta lashe wannan gasa, inda tun daga wannan lokacin ta daukaka a duniya kowa ya santa.

A shekarun baya ne matashiyar ta fara nazari akan addinai da dama amma bata samu kwanciyar hankali da addinin Kiristanci ba duk kuwa da cewa a cikin addinin aka haifeta, daga baya ta maida nazarinta kan addinin Musulunci a sannan idanunta suka bude kuma taji tana sha’awar komawa addinin na Musulunci.

KU KARANTA: Babbar magana: Na yadda akwai Allah, amma zancen wuta da aljannah kanzon kurege ne a wajena - Efia Odo

Bayan ta shafe tsawon lokaci a kasar Dubai daga baya ta yanke hukuncin komawa can da zama gaba daya.

Ta kara da cewa a lokacin da take yarinya tana ganin addinin Musulunci a matsayin addinin da bai bawa mace ‘yan ci ba amma daga baya da tayi nazari akan addinin saita ga sabanin haka.

Ta bayyana cewa ta koma Dubai da zama ne saboda ta samu karin ilimin addini.

A yayin da wannan labarin yake zuwa kuma, kwanakin baya mun kawo muku labarin wata Balarabiya 'yar asalin kasar Saudiyya da ta yi Riddah ta bar addinin Musulunci.

Balarabiyar dai ta ce ita gaba daya ma ba ta yadda akwai Allah ba, inda ta bayyana cewa rayuwar da tayi a baya rayuwa ce ta matsuwa da kuma danne mata hakki.

Budurwar ta dauki hoton kanta sanye da kayan wanka na Turawa, ma'ana dan kamfe da rigar nono, inda ta hada shi da lokacin da take sanya hijabi da niqabi tace yanzu ta fi jin dadin rayuwar ta.

To sai dai kuma mutane da yawa sun yi caa akan ta, saboda wannan abu da tayi, kuma kasar Canada ta bata takardar zama 'yar kasa ta koma can da zama za ta cigaba da zama babu addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng