Wata ta sha da kyar bayan shafe shekaru 31 a kulle wani mutumi yana lalata da ita
An kama wani mutumi da laifin tsare wata mata a gidan shi na tsawon shekaru 31, inda yake yi mata karfa-karfa yana zina da ita a kasar Venezuela
Mutumin mai suna Matias Sazalar, mai shekaru 56, ana zargin shi da keta haddin matar mai shekaru 49, da kuma mayar da ita baiwa na tsawon shekaru 31.
Wanda suka gurfanar da shi sun bayyana cewa: “Ya yaudari matar ne tun tana matashiya, inda ta bar gidansu ta biyo shi.”
Matar wacce ta shafe karni uku a cikin daki, sai dai kawai ta leko ta taga, ta saurari rediyo, sannan kuma ta kalli talabijin , kamar yadda shafin labarai na yanar gizo na kasar Venezuela mai suna Cronica Uno ya ruwaito.
Ta samu ta kubuta ne a ranar 24 ga watan Janairu, bayan Mr Salazar ya manta da mukullan gidan a cikin gidan.
Daga baya an kama Mr Salazar a cikin birnin Maracay, kusa da babban birnin Caracas, sannan an cigaba da rike shi a ofishin ‘yan sanda.
Wasu da suke zaune a kusa da inda ya tsare matar sun bayyana cewa Mr Salazar na zaune da iyalin shi a wani gida da yake kallon inda ya tsare matar.
KU KARANTA: Tirkashi: Wani mutumi da ya mutu ya tashi yayin da ake kokarin sanya shi a kabari
Da yawa daga cikinsu sun ce ba su zargi wani abu ba dangane da Mr Salazar, kawai dai sun san cewa yana da kirki.
Sai dai kuma Lauyan Mr Salazar, Jose Briceno ya bayyanawa manema labarai cewa Mr Salazar ba shi da laifi, kawai dai ana amfani da sunanshi ne a yanar gizo don jan hankalin al’umma.
Hankalin mutane ya zo kan wannan lamari ne a ranar 5 ga watan Fabrairu, a lokacin da shafin labarai na yanar gizo na Cronica Uno ya wallafa labarin.
Wani mutumi da yake zaune a kusa da gidan, da ya shiga gidan tare da matar da kuma wadanda suka gurfanar da Mr Salazar, ya bayyana cewa: “Kaya kala uku ne kawai da ita, sai wani tsohon takalmi guda daya, sai tsohon gado, tsohuwar fanka da kuma wata tsohuwar talabijin.
“Mutane sun yo caa akan mu makwabtan wajen akan mai yasa bamu kai rahoto ba, amma mu gaskiyar magana bamu san mai yake faruwa ba sai yanzu.”
A Najeriya ma dai ana samun irin wannan aika-aika inda a kwanakin baya aka samu wani mutumi a jihar Kaduna ya kulle kanwarshi a daki na tsawon shekara biyu, saboda baya son ta koma gidan mijin da ta rabu dashi.
Banda wannan kuma a Najeriya al'umma na fama da matsalar 'yan fyade masu garkuwa da mutane da dai sauransu, lamarin da a wannan lokaci babu ga mai kudi babu ga talaka, kowa ma shafar shi yake yi.
Sai dai muyi addu'ar Allah ya kawo mana sauki ya zaunar da kasar mu lafiya baki daya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng