Karin kudin Hara: Yan Najeriya zasu fuskancin karin kudin kiran waya da Data - Kamfanonin Sadarwa
Kungiyar kamfanonin sadarwan Najeriya ALTONS ta ce kamfanonin sadarwa zasu fara aiwatar da karin harajin 5.5% zuwa 7.5% daga ranar Asabar, 1 ga watan Febrairu, 2020.
Shugaban kungiyar, Gbenga Adebayo, da sakataren ayyuka, Gbolahan Awonuga, sun saki jawabin sanar da yan Najeriya kan abinda zasu fuskanta fari daga watan biyu a wannan sabuwar shekara.
Jawabin yace: "Bisa ga rattaba hannu kan dokar kudi da shugaba Muhammadu Buhari yayi.. inda ya kara kudin haraji VAT daga 5% zuwa 7.5%, kungiyar ALTON na sanar da kwastamominta cewa mambobinta (kamfanonin sadarwa) zasu fara fara aiwatarwa kan udkkan cinikayyan da za'a fari daga ranar 1 ga Febrairu, 2020."
Saboda haka, yan Najeriya zasu ga canji wajen kudn kira a waya, aika sakonni da Datan yanar gizo daga gobe.
Kamfanonin sadarwan sun tabbatarwa yan Najeriya cewa za'ayi gaskiya wajen karin da kuma aiki mai kyau.
A ranar Litinin, 13 ga watan Junairu, 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan dokar kudi domin taimaka masa wajen aiwatar da ayyuka da jawo hankulan masu sanya hannun jari.
Zaku tuna cewa Majalisar dattawan kasar ta ba ‘Yan Najeriya tabbacin cewa mutane ba za su wani ji tasirin dabbaka karin sabon tsarin harajin da za yi a kasar ba.
Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya ce wannan kari na 2.5% ba zai yi wa gama-garin ‘Yan Najeriya nauyi wajen sayen kayan da su ka saba amfani da su ba.
Ahmad Ibrahim Lawan ya nuna cewa karin da aka yi zai shafi kayan shakatawa ne da wasu kaya masu tsada, ba wadanda ake bukata a yau da kullum ba.
: “Karin harajin VAT na 2.5% ba zai shafi kayan da gama-garin ‘Yan Najeriya su ke amfani da su ba.”
“Mafi yawan kayan da aka kara masu haraji da kashi 2.5% na gayu ne wadanda akasarin mutanen kasar ba su amfani da su.” Inji Sanata Ahmad Lawan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.