http://s.rfi.fr/media/display/f0fd34f8-441d-11ea-9431-005056bfd1d9/w:1024/p:16x9/screen_shot_2020-01-31_at_12.34.42_pm.png
'Yan sanda sun kama matashin da ya yi wa kakarsa mai shekara 70 fyade a jihar FilatoDaily Trsut

Dan shekara 18 ya yi wa kakarsa mai shekara 70 fyade

by

Jami’an ‘yan sandan jihar Filato da ke Najeriya sun tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 18 bayan ya yi wa kakarsa mai shekaru 70 fyade.

Jami’an ‘yan sandan sun ce, matashin mai suna Marvellous Luka na zaune ne a kauyen Dangu-gu da ke yankin kudancin Ampang na Mangu a jihar ta Filato.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, tuni aka tuhumi matashin kuma nan kusa zai bayyana a gaban babbar kotun Pankshin domin fuskantar shari’a.

Majiyar ‘yan sandan ta ce, Luka ya amsa cewa, ya far wa kakar tasa a lokacin da take barci a dakinta, inda ya nuna mata karfi kafin lalata da ita.

Matashin ya kara da cewa, kakar ta yi ta ihun neman taimako amma ya nuna mata karfi, kafin daga bisani ya arce zuwa wata kasuwa bayan aika-aikar.

Rahotanni sun ce, matashin na aikin tura wil-baro ne a kasuwar.

A cewar Luka, shedan ne ya tura shi, kuma yana neman kakarsa da sauran al’ummar kauyen da su yi masa aikin gafara.