Ga irinta nan: An yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan ya yiwa 'yar uwar matarshi fyade

- Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yankewa wani mutum mai shekaru 37 daurin rai da rai a gidan gyaran hali

- Bayan bincike da gamsassun shaidu, kotun ta kama Francis da laifin yi wa yarinya mai shekaru 17 fyade

- Francis dai kanin mahaifiyar yarinyar ne kuma bai kalli wannan girma da dangantaka ba ya keta mata haddi

Wata kotu ta yankewa wani ma'aikacin gwamnati mai shekaru 37 hukuncin daurin rai da rai a gidan gyaran hali. Wanda aka yankewa hukuncin mai suna Francis Yusuf Kyamang ya samu wannan hukuncin ne sakamakon fyade da yayi wa karamar yarinya a Abuja, kamar yadda jaridar Information Nigeria ta ruwaito.

An yankewa mutumin mai suna Francis Yusuf Kyamang hukuncin ne a ranar Talata a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Mai shari'a Hassan Babangida ne ya kama shi da laifin bayan an tabbatar da abinda ake zargin shi da shi. Francis dai ya yi wa yarinya mai shekaru 17 fyade ne a Abuja.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/dd342920394678df.jpeg
Ga irinta nan: An yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan ya yiwa 'yar uwar matarshi fyade
Source: Facebook

Amma kuma Francis Yusuf Kyamang ya kasa bayyanawa kotu dalilin shi na yin wannan mummunan aikin a kan diyar yayan shi.

Ba yanzu aka fara samun irin wannan mummunar dabi'ar ta fyade ba. A kan samu wasu manyan kawai su haye yara masu kananan shekaru tare da lalata su.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta ruwaito yadda wata yarinyar mai matsalar ji ta suma a gaban kotu bayan da ta ga wanda yayi mata fyade.

KU KARANTA: San barka: El-Rufai ya karawa 'yan fansho kudi zuwa naira dubu talatin

Yarinyar mai shekaru 13 ta fadi sumamma ne a gaban kotu bayan da alkali ya kira mutumin da ake zargi da yi mata fyade.

Ta fashe da kuka tare da nuna shi tana kokarin magana amma sai ganinta aka yi a kasa warwas. Da taimakon lauyoyi da 'yan sanda aka fitar da ita bayan an tsayar da sauraron shari'ar.

Masana halayyar dan Adam da suka kware wajen bada shawara ne suka lallaba yarinyar a kan ta kwantar da hankalinta don a gaban kotu take.

Bayan dawowa hutun ba-zata da aka yi, alkalin yayi kira ga yarinyar da ta kwantar da hankalinta don ba shakka za a kwatar mata hakkinta. A nan ne ta bayyana cewa mutumin dai shine mamallakin makarantar da tayi kuma yayi lalata da ita kusan sau biyar. Yana mata barazana da wuka a kan cewa zai yanka ta idan ta sanar da mahaifiyarta.

Wata rana ne dubun shi ta cika kuma mahaifiyarta ta kama shi a kanta, dalilin da yasa ta kai kara gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng