http://s.rfi.fr/media/display/aaf8e118-440a-11ea-8f0b-005056a98db9/w:1024/p:16x9/ae0cc0c15e75a3851447555e0d582f59369931c5.jpg
Wasu nau'ukan makamaiAFP Photo/ASHRAF SHAZLY

An yi amfani da makaman Al Qaeda wajen kai hari a Najeriya

by

Binciken da wata kungiya da ke birnin London ta gudanar ya nuna cewa, makaman da aka yi amfani da su a rikicin makiyaya da maonma a arewa maso yammacin Najeriya, tushensu daya da makaman da mayakan al Qaeda suka yi amfani da su a hare-haren kasashen yankin Sahel.

Rahoton Kungiyar ta Conflict Armamnet Reasearch (CAR) ya mayar da hankali ne kan tashe-tashen hankulan jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.

Mike Lewis, shugaban kungiyar CAR ya shaida wa Radio France International cewa, sun gano cewa, makaman da aka yi amfani da su a Najeriyar, iri daya ne da wanda ‘yan ta’adda suka yi amfani da su a farmakin Mpoti da ke kasar Mali.

Kazalika rahoton ya kara da cewa, an yi safarar miyagun makamai ta ruwa daga kasar Turkiya zuwa Najeriya .

Lewis ya kara da cewa, ba lallai ba ne maharan sun yi amfani da makamai iri daya sak wajen kaddamar da mabanbantan hare-hare a kasashen Sahel, amma tabbas sun samo asli ne daga tushe guda.