San barka: El-Rufai ya karawa 'yan fansho kudi zuwa naira dubu talatin
- Kungiyar 'yan fansho reshen jihar Kaduna ta jinjinawa Gwamna Nasir El-Rufai a kan karin kudin fansho da yayi zuwa mafi karancin albashi na dubu talatin
- Shugaban kungiyar ya bayyana cewa hakan na nuna cewa gwamnan ya damu da walwala da farin cikin tsofaffi da dattijan jihar
- Gwamnan ya bayyana cewa karin karancin fanshon zuwa dubu talatin din zai kara yawan kudin albashin ma'aikatan jihar da naira miliyan 200
Kungiyar 'yan fansho reshen jihar Kaduna ta jinjinawa Gwamna Nasir El-Rufai da ya kara musu karancin fansho a jihar zuwa naira dubu talatin a duk wata.
Kungiyar ta ce gwamna El-Rufai ne gwamnan farko da ya sanar da fara biyan karancin fansho kuma hakan na nuna cewa ya damu da walwala da jin dadin dattijan jihar.
Kamar yadda takardar da mai bada shawara na musamman a kan yada labarai ga gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye ya fitar, ya ce kungiyar ta jinjinawa Gwamna El-Rufai ta wasikar da shugaban kungiyar, Alhaji Abdu Ramalan Kwarbai yasa hannu.
Kamar yadda NUP ta bayyana, hukuncin El-Rufai na kara kudin fanshon "ya nuna damuwar shi da walwalar tsofaffi da dattijan jihar Kaduna."
Kungiyar 'yan fanshon ta mika godiyarsu ga gwamnan kasancewar shi na farko da ya fara biyan karancin albashi a kasar nan, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
KU KARANTA: Jerin jihohi 15 da suka fi cin bashi a Najeriya
Idan zamu tuna, gwamnan yayi alkawarin daga kudin fanshon a wata tattaunawa da aka yi kwanan nan da shi a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Kamar yadda El-Rufai ya sanar, ya sha matukar mamaki ta yadda wasu 'yan fansho ke karbar naira dubu uku zuwa dubu bakwai a duk wata. Ya ce ba zai lamunci hakan ba kwata-kwata.
A take kuwa gwamnan yayi alkawarin karin kudin fanshon ga tsofaffin ma'aikatan jihar kuma zai mika lamarin gaban majalisar jihar. Za a kuma fara biyan karancin fanshon a lokacin da suka amince.
El-Rufai ya ce duk da karancin fanshon zai kawo kari a kudin biyan ma'aikatan jihar Kaduna da naira miliyan 200, amma dole ne tsofaffin ma'aikatan jihar Kaduna su zauna cikin walwala da farin ciki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng