'Yan PDP 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a Zamfara - Jaji

Tsohon shugaban jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar Maradun na jihar Zamfara Alhaji Bala Roka ya fice daga jamiyyar ya koma jamiyyar APC tare da magoya bayansa kimanin 3,000.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Aminu Sani Jaji ne ya bayar da sanarwar.

Jaji ya yi wannan sanarwar ne jiya a birnin tarayya Abuja inda ya ce tsohon shugaban karamar hukumar ya jagoraci wadanda suka sauya shekan zuwa APC ne kwanaki biyu bayan kotun koli ta tabbatarwa Gwamna Bello Matawalle nasararsa a matsayin hallastacen zababen gwamnan jihar.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/18700d0dd20c8ea0.jpg
'Yan PDP 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a Zamfara - Jaji
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wani da su kayi karatu tare da Maryam Sanda ya fadi irin halayenta da ya sani

A wani rahoton, mun kawo muku cewa a ranar Alhamis ne shugabannin jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya, reshen jihar Kebbi suka koma jam'iyyar APC a jihar.

Shugaban matasan Kwankwasiyya na jihar, Mohammed I. Anaruwa Kele, wanda yayi magana a madadin masu canza shekar a Birnin Kebbi, ya ce hukuncin barin jam'iyyar ya biyo bayan tsananin biyayyarsu ne ga shugaban darikar Kwankwasiyya, Rabiu Suleiman Bichi.

Ya ce a lokacin da suka gano cewa shugabansu ya bar Kwankwasiyya, ba su kara wani tunani ba da ya wuce na komawa jam'iyyar APC din, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda yace, shugabannin Kwankwasiyyar sun amince da barin jam'iyyar ne ganin cewa burinsu da biyayyarsu ta ginu ne da ganin sun bada gudummawa wajen ci gaban damokaradiyya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng