An kashe mutane 3, an babbaka gidaje 20 saboda rikicin sarauta a jahar Kogi
Akalla mutane uku ne suka mutu a sakamakon wata rikita rikita da ta kunno kai a kan wata kujerar sarauta a cikin karamar hukumar Ankpa ta jahar Kogi, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu gidajen sarauta guda biyu ne suke jayayya a kan wannan kujerar sarauta wanda aka dade ana zaban wanda zai hauta a tsakaninsu, toh amma a wannan karo lamarin ya ta’azzara, har ta kai ga zubar da jini da asarar dukiya.
KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kaduna ta yi nadin sabon shugaba a hukumar jin dadin alhazai
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne a daren Laraba, 29 ga watan Janairu a kan wannan kujerar sarauta ta ‘Onu Akwu’, sai dai ba daga ranar aka fara jayayyar ba, sun dade kowa na ikirarin lokacinsa ne ya fitar da sarki, wanda har ta kai su ga kotu.
“Muna cikin barci sai muka ji hayaniya daga yankin gabashin garinmu, a lokacin da na fito sai na tarar wasu gidaje suna ci da wuta.” Kamar yadda wani mazaunin garin, kuma ganau ba jiyau bay a bayyana.
Wannan ganau ya kara da cewa: “Akalla gidaje 20 aka kona a daren, kuma mun dauke gawarwaki guda 3, haka nan mun kwashe mutane da dama wadanda suka samu rauni tare da mikasu ga asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a Ankpa da makwabtan.”
Daga cikin gidajen da aka kona akwai gidan shugaban riko na karamar hukumar Ankpa, John Aduga, wanda majiyoyi suka tabbatar akwai dan uwansa daga cikin masu takarar darewa wannan kujerar sarauta ta ‘Onu Akwu”.
A wani labarin kuma, Wata mata mai suna Ngodoo ce ta gamu da ajalinta bayan ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take tsaka da raba fada tsakanin yaranta biyu, namiji da kanwarsa.
Daily Trust ta ruwaito wannan lamari mai ban ta’ajibi ya faru ne a gidanta dake kan titin sabon kasuwan zamani a cikin garin Makurdi, babban birnin jahar Benuwe a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu.
Rahotanni sun bayyana cewa matar, wanda ta kammala shirin fara karatun digiri na uku a jami’ar noma ta gwamnatin tarayya dake Makurdi ta rasu ne a daidai lokacin da danta dan shekara 28 yayi kokarin daba ma kanwarsa wuka.
Haka zalika rahotannin sun bayyana cewa dan matar mai suna Dominic ya yi kaurin suna a unguwarsu a matsayin mai yawan neman fada, kuma dan daba, wanda hakan ya dade yana ci ma babarsa tuwo a kwarya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa